Belin N500m: Kotu Ta ba Saki Yahaya Bello, An Kafa Masa Sharuda Masu Tsauri
- Kotun tarayya da ke Abuja ta bai wa tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, belin Naira miliyan 500 tare da kafa wasu sharuda
- An umurci Yahaya Bello da ya mika fasfon sa na kasa da kasa tare da dakatar da tafiye-tafiye zuwa waje ba tare da izini ba
- An tsayar da ranakun 24 da 28 ga Fabrairu domin fara sauraron shari’ar kan wasu zarge zarge da EFCC ke yi wa tsohon gwamnan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kotun tarayya da ke birnin Abuja ta bai wa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello belin Naira miliyan 500 bayan zaman kotu da aka yi a ranar Juma’a.
Alkalin kotun, Mai shari’a Emeka Nwite, ya ce dole masu tsaya masa a kan belin su kasance suna da filaye a Abuja tare da gabatar da takardun mallakar su domin tantancewa.
Vanguard ta wallafa cewa an umurci Yahaya Bello da ya zauna a kurkukun Kuje har sai ya cika sharuddan belin da kotu ta gindaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
N500m: Sharuddan belin Yahaya Bello
Kotun ta ce masu tsaya wa Yahaya Bello dole su gabatar da shaidar mallakar filaye a Abuja tare da gabatar da hoton fasfo.
Rahoton Channels Television ya nuna cewa an umurce su da su tabbatar da bin duk sharuddan belin kafin a saki Yahaya Bello daga gidan yarin Kuje.
An dakatar da tafiye-tafiyen Yahaya Bello
Kotun ta nemi Yahaya Bello da ya mika fasfon sa na kasa da kasa, tare da dakatar da duk wani shirin fita zuwa kasashen waje ba tare da izinin kotu ba.
Wannan matakin ya zo ne domin tabbatar da cewa Yahaya Bello yana nan a Najeriya domin fuskantar shari’ar da ake masa.
Za a gurfanar da Yahaya Bello a Fabrairu
Kotun ta tsayar da ranakun 24 da 28 ga Fabrairun shekarar 2025 domin fara sauraron shari’ar da EFCC ta gabatar a kan zargin almundahanar Naira biliyan 80.2.
An zargi Yahaya Bello da yin amfani da wasu mutane biyar wajen siyan kadarori masu tsada a Abuja da birnin Dubai yayin da yake gwamna daga 2016 zuwa 2024.
EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan Kwara
A wani rahoton, kun ji cewa babbar kotu a Kwara ta cigaba da sauraron shari'ar da EFCC ta shigar da tsohon gwamnan jihar, AbdulFatah Ahmed.
Legit ta ruwaito cewa hukumar EFCC kasa ta maka AbdulFatah Ahmed a gaban kotu bisa zargin lamushe kudin da suka kai Naira biliyan biyar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng