Jami'in Gwamnati Ya Yi Tone Tone, Ya Fallasa Yadda Tsohon Gwamna Ya Wawure N5bn
- Babbar kotun jihar Kwara ta cigaba da sauraron shari'ar da EFCC ta shigar gabanta a kan tsohon gwamnan Kwara, AbdulFatah Ahmed
- Hukumar da ke yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta maka AbdulFatah Ahmed a gaban kotu bisa zargin lamushe kudin makaranta
- Hukumar ilimin firamare ta kasa ta fitar da kudaden a shekarun 2013, 2014 da 2015 domin a inganta makartun firamare da karamar sakandare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Kwara - Mataimakin daraktan kudi na hukumar ilimin bai daya (UBEC), Abubakar Hassan, ya bayyana a kotu don bayar da shaida a kan zargin tsohon gwamnan Kwara da almundahana.
Ana zargin tsohon gwamna, Abdulfatah Ahmed da kwamishinansa na kudi, tare da wasu mutane da almubazzaranci da kudaden da aka ware domin biyan albashin malamai.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa a zaman da aka cigaba da yi kan zargin a gaban Mai Shari’a Mahmud Abdulgafar na babbar kotun Kwara, EFCC ta gabatar da shaidanta na farko.
Kwara: An zargi gwamna da wawashe N5bn
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa shaidan EFCC, Abubakar Hassan, ya fadawa kotu abin da ya sani na yadda aka yi almubazzarancin kusan N5bn na biyan malaman UBEC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa an ware kudin domin aiwatar da ayyuka a makarantun firamare da karamar sakandare tsakanin shekarun 2013 da 2015, lokacin da Ahmed ke mulki a matsayin gwamna.
An zargi tsohuwar gwamnatin Kwara da almundahana
Shaidan EFCC ya shaidawa kotu cewa UBEC ta tura kudade ga gwamnatin Kwara a shekarar 2013, 2014 da 2015.
Abubakar Hassan ya kara da cewa;
"Jihar Kwara ta samu kimanin Naira biliyan biyar a 2013, Naira miliyan 876 a 2014, da Naira miliyan 982 a 2015, wanda ya kama kusan Naira biliyan biyar gaba daya."
Ya bayyana cewa babu wani aiki da aka yi a 2016, 2017 da 2018 saboda gazawar jihar duk da shawarwarin da hukumar UBEC ta bayar na tabbatar da an gudanar da ayyukan.
Gwamnatin Kwara ta yi bayanin albashin ma'aikata
A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Kwara ta yi bayani a kan dalilin da ya sa wasu daga cikin ma'aikatan jihar ba su samu albashinsu na watan Nuwamba, 2024 ba.
Kwamishiniyar kudi ta jihar, Hauwa Nuru, ta bayyana cewa ma’aikatan da abin ya shafa ba su kammala rajista da hukumar KWSRRA kamar yadda takwarorinsu suka yi ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng