'Yan Bindiga Sun Fara Gwajin Bama Bamai a Zamfara, Yaran Bello Turji 2 Sun Mutu

'Yan Bindiga Sun Fara Gwajin Bama Bamai a Zamfara, Yaran Bello Turji 2 Sun Mutu

  • 'Yan bindiga biyu sun mutu yayin gwajin bama bamai a sansanin Bello Turji da ke karamar hukumar Talata Mafara, jihar Zamfara
  • An rahoto cewa Bello Turji ya samu karin bama bamai da aka kawo masa a kan rakuma, da nufin kara yawaitar hare-harensa
  • Fashewar bam din da ta kashe 'yan bindigar ta tilasta mazauna Garin Gwale guduwa daga gidajensu saboda tsoron hare-haren

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - 'Yan bindiga biyu sun bakunci lahira yayin gwajin abubuwan fashewa (IED) a wani sansanin Bello Turji da ke jihar Zamfara.

Fashewar ta samo asali ne daga kuskuren gwajin bam din da ‘yan bindigar suka yi karkashin jagorancin wani na hannun daman Bello Turji mai suna Dogo Auta.

'Yan bindiga sun yi gwajin bama bamai, an samu asarar rayuka a Zamfara
'Yan bindiga 2 sun mutu yayin da suke gwajin bama bamai a jihar Zamfara. Hoto: Legit.ng Hausa
Asali: Original

Bello Turji ya karbi bama bamai a Zamfara

Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa lamarin ya faru ne a tsakanin Barikin Daji da tsaunukan Dan Bagudu da ke karamar hukumar Talata Mafara.

Kara karanta wannan

Gwamna zai tura mata 1,000 karatu fannin lafiya, zai raba kwamfutoci miliyan 1

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar mai sharhi kan lamuran tsaron ta tabbatar da cewa Bello Turji ya karbi wasu bama baman IED da aka kawo sansaninsa ta hanyar amfani da rakuma.

An ce Bello Turji ya karbi wadannan bama bamai ne domin kara yawaita kai hare hare a garuruwan Arewa maso Yamma kamar yadda ya yi alkawari.

Fashewar bam ta jefa mutane a firgici

Fashewar bam din ta jefa tsoro cikin jama’a a garuruwan da ke kusa, ciki har da Garin Gwale, inda mutane suka fara guduwa saboda tsoron hare-hare.

Majiyoyin sun bayyana cewa kungiyoyin ‘yan bindiga na amfani da bama baman IED don kai hare-hare kan sojoji da fararen hula a Zamfara, Sokoto da makotansu.

An gargadi jami’an tsaro da su kasance cikin shirin ko ta kwana saboda yiwuwar hare-hare a nan gaba bayan mallakar bama baman da Bello Turji ya yi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun rikita gari da harbi, sun bi gida gida sun dauki mata da yara

'Yan bindiga sun sace amarya da kawayenta

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan bindiga masu biyayya ga Bello Turji a jihar Sokoto sun tarwatsa 'yan biki tare da sace amarya da wasu kawayenta hudu.

An ce lamarin ya faru ne a Kwaren Gamba da ke kusa da Kuka Teke, inda 'yan bindigar suka bude wuta kan mai uwa da wabi kafin arcewa da sabuwar amaryar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.