'Ko ba PVC za a yi Zabe,' INEC Ta Fitar da Sababbin Tsare Tsare

'Ko ba PVC za a yi Zabe,' INEC Ta Fitar da Sababbin Tsare Tsare

  • Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce za a sauya dokokin amfani da katin PVC domin samar da sauƙin kada ƙuri’a
  • INEC ta fitar da shawarwari 142 data samu bayan zaɓen 2023, ciki har da batutuwan gyaran tsarin zaɓe da ilmantar da masu zabe
  • Shawarwarin sun haɗa da amincewa da zaɓe daga ketare, masu taya INEC aiki a lokacin zaɓe da gyaran rajistar masu kada ƙuri’a

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban hukumar zaɓe ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce bai kamata yin amfani da katin zaɓe na PVC kadai ya zama ka’ida ɗaya tilo ta tantance masu zaɓe ba.

Shugaban INEC ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wani taro tare da kwamishinonin zaɓe na jihohin Najeriya a Abuja.

Kara karanta wannan

'Sun fara shirin murde zabe,' Farfesa Jinadu ya tono zargin magudi a 2027

Zaben Najeriya
INEC ta fitar da sababbin tsare tsaren zabe. Hoto: INEC Nigeria
Asali: Twitter

Vanguard ta wallafa cewa Farfesa Yakubu ya ce shawarwarin da suka fito daga rahoton nazari kan zaɓen 2023 sun nuna bukatar sababbin hanyoyin da za su inganta tsarin zaɓe a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauya fasalin zabe da katin PVC

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce bayan fara aiki da fasahar BVAS, katin PVC ba zai kasance tilas domin tantance masu kada ƙuri’a ba.

INEC za ta fara amfani da takardun da ake bayarwa idan aka yi rajistar PVC, wadanda za a iya sauke su daga shafin hukumar domin tantance masu kada ƙuri’a.

Ya ce wannan tsarin zai rage wahalar karɓar katunan zaɓe da kuma magance matsalar rashin katunan PVC wajen hana wasu kada ƙuri’a.

Shirye-shirye ga masu aiki lokacin zaɓe

Shawarwarin sun kuma haɗa da bai wa ma’aikatan INEC, jami’an tsaro, masu sa ido, da ‘yan jarida damar kada ƙuri’a yayin zaɓe.

Kara karanta wannan

Karfin Naira: Ƴan canji sun lissafa abubuwa 3 da suka jawo dalar Amurka ta karye

Leadership ta wallafa cewa an gabatar da shawarwari kan bai wa ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje damar kada ƙuri’a.

Inganta rajista da yawan masu zabe

A cewar hukumar, INEC za ta yi aiki tare da hukumar kula da shaidar dan kasa (NIMC) da hukumar kididdigar jama’a (NPC) domin tsaftace rajistar masu zaɓe.

Farfesa Yakubu ya ce akwai bukatar fadada ilimin zaɓe domin yaki da labaran ƙarya da bayanan da ba su dace ba.

Haka zalika, hukumar za ta ci gaba da gudanar da gyaran tsarin zaɓe domin tabbatar kowane dan kasa ya kada kuri'a.

An fara zargin magudi a zaben 2027

A wani rahoton, kun ji cewa Fafesa Adele Jinadu ya yi zargin cewa 'yan siyasa sun fara shirye-shiryen magudin zaɓen shekarar 2027.

Farfesa Adele Jinadu ya yi zargin cewa sayen ƙuri'u da tikitin takara sun zama ruwan dare a Najeriya kuma hakan bai dace da tsarin gaskiya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng