Hankula Sun Tashi bayan Fashewar Wani Bam a Borno, Bayanai Sun Fito

Hankula Sun Tashi bayan Fashewar Wani Bam a Borno, Bayanai Sun Fito

  • An samu asarar rayukan bayan wani abin fashewa ya tashi a wani ƙauye da ke jihar Borno da ya yi fama da ta'addanci
  • Wannan bam da ya tashi a wani rukunin gidaje da ake ginawa, ya yi sanadiyyar rasuwar mutum biyu har lahira
  • Fashewar bam ɗin dai ta auku ne a daidai lokacin da Gwamna Babagana Umara Zulum ke ƙaddamar da wani aiki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - An samu tashin bam a wani rukunin gidajen da ake ginawa a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya

Rahotanni sun bayyana cewa tashin bam ɗin ya yi sanadiyyar rasuwar mutane biyu a wani rukunin gidaje 200, da ake ginawa a garin Dalwa na jihar Borno.

Bam ya fashe a Borno
Bam ya tashi a wani rukunin gidaje a Borno Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Tashar Channels tv ta rahoto cewa tashin abin fashewar ya auku ne da misalin ƙarfe 1:00 na rana a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Hankalin fasinjoji ya tashi,jirgin sama ya samu matsala yana shirin sauka a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An samu tashin bam a jihar Borno

Tashin bam ɗin dai ya auku ne a daidai lokacin da gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum da takwaransa na Yobe, Mai Mala Buni, suke ƙaddamar da rukunin gidaje a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Wata majiya ta bayyana cewa irin wannan lamarin ya faru a ranar Talata amma babu cikakken bayani kan fashewar ta ranar Talata.

Garin Dalwa dai na da tazarar kilomita 175 daga Maiduguri kuma yana ɗaya daga cikin ƙauyukan da ƴan ta'addan Boko Haram suka lalata tare da raba mutanen da ke rayuwa a wajen da muhallansu.

Gwamna Babagana Umara Zulum ya fara aikin sake gina garin Dalwa da gidaje guda 200.

Me ƴan sandan jihar Borno suka ce?

Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Borno, ASP Nahum Daso domin samun ƙarin bayani kan lamarin

Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa yana jiran rahoto ne daga DPO na yankin kan abin da ya faru a wajen.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi wa'azi ana alhinin rasuwar shugaban karamar hukuma

"Na tuntuɓi DPO na yankin, ina jiransa domin samun bayanai, saboda har yanzu ban samu rahoto daga gare shi ba."

- ASP Nahum Daso

An mutu da bam ya tashi a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa aƙalla mutane 10 ne suka rasa ransu sakamakon tashin wani bam da ake zargin mayaƙan ISWAP ne suka dasa a titin Baga-Kukawa.

Lamarin ya faru ne a lokacin da wata motar bas ta taka Bam ɗin, wanda ya jawo rasuwar mutanen yayin da wasu kusan mutum 20 suka samu raunuka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng