Shugaban Kasar Jamus Ya Sauka a Najeriya, Zai Gana da Tinubu

Shugaban Kasar Jamus Ya Sauka a Najeriya, Zai Gana da Tinubu

  • Shugaban kasar Jamus, Frank-Walter Steinmeier, ya sauka a Najeriya inda zai gudanar da ziyarar kwanaki biyu
  • A zaman da zai yi, ana sa ran zai tattauna da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da kuma shugaban ECOWAS
  • Daga nan Mista Frank-Walter Steinmeier zai ziyarci daya daga cikin jihohin kasar nan domin gana da 'yan kasuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Shugaban kasar Jamus, Frank-Walter Steinmeier, ya isa Fadar Gwamnati ranar don ziyartar shugaba Bola Tinubu.

Tun a ranar Talata shugaban ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe, Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya tarbe shi.

Jamus
Shugaban Jamus ya sauka a Najeriya Hoto: @ikwerre
Asali: Twitter

A sakon da hadimin shugaban kasa, Dele Alake ya wallafa a shafinsa na X, an gano Mista Steinmeier, ya na samun tarba ta musamman daga jami’an kasar nan.

Kara karanta wannan

A karo na 6, kotu ta sake ingiza keyar Mama 'Boko Haram' zuwa kurkuku

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ayyukan da shugaban Jamus zai yi a Najeriya

Jaridar Channels ta wallafa cewa shugaban kasar Jamus, Frank-Walter Steinmeier, zai gana da shugaba Bola Ahmed Tinubu a kan batun da ya shafi alakar kasashen biyu.

Haka kuma zai gana da Shugaban hukumar kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS), Alieu Omar Touray, da wasu mutane.

Ziyarar da shugaban Jamus ya kawo Najeriya za ta zo karshe ne a ranar 12 Disamba, 2024, kamar yadda gwamnati ta sanar.

Shugaban kasar Jamus zai wuce Legas

Ana sa ran bayan ya kammala ayyukansa a babban birnin tarayya Abuja, Mista Steinmeier, zai wuce zuwa jihar Legas.

Da saukarsa a jihar, zai gana da wakilan ‘yan kasuwa, zai ziyarci cibiyar hada-hadar 'yan kasuwa, sannan ya hadu da wakilai a bangaren al’adu da kungiyoyin farar hula na Najeriya.

Bashin Jamus ya dabaibaye Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa kasar nan ta kara shiga cikin matsalar bashi bayan an samun karuwar basussuka daga kasashen Turai; ciki har da Faransa da Jamus.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun soki kalaman Sakataren Gwamnati kan takara da Tinubu a 2027

Rahoton ofishin kula da basussuka na kasa ya ce kasar China da Faransa da Jamus, Japan da wasu kasashen duniya su na bin Najeriya bashin da ya kai Dala bilyan biyar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.