Hotuna: Fitaccen Mawakin Siyasar Arewa, Rarara Ya Fara Gina Sabon Masallaci a Kano
- Mawaki Dauda Kahutu Rarara ya fara gina sabon masallaci a garin Kuduri da ke karamar hukumar Sumaila, jihar Kano
- A cewar sanarwar Rabi’u Garba Gaya, mutanen Kuduri sun nemi taimakon mawakin bayan ruwan sama ya rushe masallacinsu
- Rarara ya amsa rokon mutanen, ya tura wakilinsa Mallam Abdullahi Alhikimah domin kaddamar da ginin sabon masallacin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Fitaccen mawakin siyasar Arewa, Dauda Kahutu Rarara ya fara gina sabon masallaci a garin Kuduri da ke cikin karamar hukumar Sumaila, jihar Kano.
A kwanakin baya ne al'ummar garin Kuduri suka kai wa Rarara ziyarar ban girma sannan suka nemi mawakin ya gina masu masallaci a garinsu.
Al'ummar Kuduri sun nemi taimakon Rarara
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Rabi'u Garba Gaya, mai magana da yawun Rarara ya fitar a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rabi'u Gaya ya sanar da cewa al'ummar garin Kuduri sun shaidawa mawaki Rarara cewa ruwan sama ya rushe masu masallacinsu.
"Al'ummar garin Kuduri da ke karamar hukumar Sumaila sun ci gaba da cewa a lokacin damuna ruwa ya rushe masallacinsu, don haka suke roko a gina masu wani."
- A cewar sanarwar Rabi'u Gaya.
Rarara ya fara gina sabon masallaci a Kuduri
Sanarwar ta ci gaba da cewa, mawakin ya amsa rokon al'ummar garin Kuduri inda ya ba da umarnin gina wani masallacin.
"Yau cikin yardar Allah, abokinsa Mallam Abdullahi Alhikimah ya wakilce shi zuwa kaddamar da sake ginin masallacin.
"Al'ummar garin Kuduri sun yiwa mawaki Alhaji Dauda Kahutu Rarara godiya tare da fatan Allah ya rabashi da mahaifiyarsa lafiya."
- A cewar Rabi'u Gaya.
Kalli hotunan a kasa:
Rarara zai gina masallacin N350m a Katsina
A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen mawaki, Daudada Kahutu Rarara ya ware Naira miliyan 350 domin gina katafaren masallacin Juma'a a Katsina.
Mawaki Rarara zai gina masallacin ne a mahaifarsa Kahutu da ke karamar hukumar Danja, jihar Katsina, lamarin da ya jefa mutanen garin a cikin farin ciki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng