An Kama Masu Taimakon 'Yan Bindiga da Kayan Sojoji da 'Yan Sanda

An Kama Masu Taimakon 'Yan Bindiga da Kayan Sojoji da 'Yan Sanda

  • Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama mutane da ake zargi da kai kayan sojoji ga ‘yan bindiga a jihar Katsina
  • Kayayyakin da aka gano sun haɗa da kakin sojoji da na ‘yan sanda, wanda ake zargin za a bai wa ‘yan bindiga masu garkuwa
  • Rahotanni sun nuna cewa wadanda ake zargin sun amince da laifin kuma kwamishinan 'yan sanda ya fadi matakin da za su dauka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Rundunar ‘yan sandan Katsina ta kama wani mutum mai suna Aminu Hassan, mai shekaru 25 daga Dundubus, ƙaramar hukumar Daja.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ana zargin Aminu Hassan da tallafa wa ‘yan bindiga a Danmusa da kewaye.

Kayan sojoji
An kama masu taimakon 'yan bindiga da kayan sojoji. Hoto: Katsina State Police Command
Asali: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa an kama Aminu Hassan dauke da kakin sojoji da aka ɓoye a cikin leda yayin sintiri a kan titin Yantumaki da Kankara ranar 19 ga Nuwamba, 2024.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun rikita gari da harbi, sun bi gida gida sun dauki mata da yara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan bincike, an kama wasu mutane 3 da ake zargi da hannu a aika-aikar: Lawal M Ahmad, Isma’il Dalhatu, da Shafi’u Adamu.

Adadin kayan sojoji da aka kama

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Katsina, ASP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa an gano kayan sojoji guda 14 da na ‘yan sanda guda ɗaya a hannun waɗanda ake zargi.

Rahoton Channels Television ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu na kai kayan sojoji ga ‘yan bindiga domin amfani da su wajen aikata laifuffuka.

Jawabin kwamishinan 'yan sanda

Kwamishinan ‘yan sanda na Katsina, CP Musa Aliyu ya yaba wa jami’an rundunar bisa ƙoƙarinsu na kama waɗanda ke aikata laifuffuka a jihar.

Ya kuma yi kira ga al’umma su ci gaba da ba da bayanai masu muhimmanci da za su taimaka wajen yaƙi da aikata laifuffuka a jihar.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun yi fatali da kudin fansa, sun fadi dalilin raina Naira miliyan 3

CP Musa Aliyu ya ce za su ci gaba da aiki ba dare ba rana domin tabbatar da tsaron dukkan mazauna jihar Katsina.

An sace mutane 43 a jihar Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan bindiga sun kai hari a kauyen Kakidawa da ke yankin Gidan Goga a jihar Zamfara.

An ruwaito cewa 'yan bindiga masu garkuwa da mutanen sun sace mutane 43 a yankin wanda kuma mafi yansu mata ne da yara kanana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng