Bayan An Samu Asarar Rayuka, Mazauna Kano Sun Shiga Fargabar Dawowar Fadan Daba

Bayan An Samu Asarar Rayuka, Mazauna Kano Sun Shiga Fargabar Dawowar Fadan Daba

  • Mazauna wasu daga cikin unguwannin jihar Kano sun fada zaman dar-dar saboda fargabar dawowar fadan daba
  • Wuraren da ke cikin matsananciyar fadan daba sun hada da unguwannin Zango da Yakasai da ke kusa da Kasuwar Rimi
  • Sai dai rundunar 'yan sandan jihar ta jaddada matsayarta na tabbatar da cewa an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Mazauna birnin Kano sun fara shiga halin zaman dar-dar bayan fadan daba ya salwantar da rayuwar mutane biyu.

A kwanakin nan ne aka kaure da fadan daba bayan wasan kwallon kafa a filin wasa na Sani Abacha da ke unguwar Kofar Mata.

Kwamishina
Mazauna Kano sun shiga fargaba sabo da fadan daba Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa ‘yan daban sun farmaki unguwannin Zango da Yakasai da ke kusa da Kasuwar Rimi, su ka rika yin kwace.

Kara karanta wannan

A karo na 6, kotu ta sake ingiza keyar Mama 'Boko Haram' zuwa kurkuku

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An samu rahoton cewa ‘yan dabar sun farmaki wata ma’aikaciyar jinya a asibitin kwararru na Murtala Muhammad.

Mazauna Kano sun tsorata da harkar daba

Aisha Gwani, mazauniyar Yakasai ce, ta shaida wa Legit cewa har fargaba su ke a fara fadan daba.

“Har shela su ke yi mana a aiko da wasika a ce za a shigo gari, kuma in dai sun ce za su shigo, sai sun zo.”

Ta bayyana cewa ba a fadan daban da ya wakana a makon da ya gabata ne aka fara fadan dabar ba, ta ce tun kimanin watani biyu ake ta gwabzawa.

Martanin ‘yan sanda ga fadan daban Kano

Rundunar ‘yan sandan Kano ta bayyana cewa a tsaye ta ke wajen yaki da fadan daba a dukkanin fadin jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ya wallafa da a shafinsa na Facebook cewa dukkanin mazauna unguwannain Kano sun san ‘yan daba da masu sayar masu da kwayoyi.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun soki kalaman Sakataren Gwamnati kan takara da Tinubu a 2027

Kano: Kwamishina ya tafi farautar 'yan daba

A wani labarin, kun ji cewa kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Salman Dogo Garba ya yi tattaki da kansa zuwa wasu daga cikin unguwannin jihar da ake fama da fadan daba.

CP Salman Dogo Garba ya mika bukatar neman hadin kai da taimakon jama'a, domin a cewarsa, ta haka ne za a samu nasarar magance matsalar daba da ke kokarin dawowa jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.