Makiyaya Sun Kwace Bindigar Wani Babban Soja, An Cafke Shugaban Miyetti Allah

Makiyaya Sun Kwace Bindigar Wani Babban Soja, An Cafke Shugaban Miyetti Allah

  • Dangin Bello Bodejo, shugaban kungiyar Miyetti Allah sun yi ikirarin cewa sojojin Najeriya sun cafke shi ba tare da wani laifi ba
  • An ce Bello Bodejo ya yi kokarin sasanta wani rikici da ya afku tsakanin makiyaya da wani soja a Tudun Wada amma aka tsare shi
  • Dangin Bodejo sun yi kira ga shugaban sojoji da hukumomi da su gudanar da bincike na gaskiya da sakin Bello Bodejo nan take

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Nasarawa - Dangin shugaban kungiyar Miyetti Allah, Bello Bodejo, sun bayyana cewa sojojin sojojin Najeriya sun cafke Bodoje tare da tsare shi.

Suleiman Waziri, dan uwan Bodejo, ya ce sojojin bataliya ta 117 ne suka kama shugaban Miyetti Allah a ranar Talata a ofishinsa da ke Maliya, jihar Nasarawa.

Dabgin Bello Bodejo sun yi magana yayin da sojoji suka cafke shugaban Miyetti Allah
Sojoji sun cafke shugaban Miyetti Allah kan hatsaniya tsakanin makiyaya da wani janar. Hoto:Bello Bodejo, HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Sojojin Najeriya sun cafke Bello Bodejo

Kara karanta wannan

A karo na 6, kotu ta sake ingiza keyar Mama 'Boko Haram' zuwa kurkuku

A wani rahoto na The Cable, Waziri ya ce an kama Bodejo ne saboda wata hatsaniya da ta faru tsakanin makiyaya da wani janar mai ritaya a Tudun Wada, Nasarawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Suleiman Waziri ya sanar da cewa:

“A Ranar 8 ga Disamba 2024, wani janar ya harbe shanu a Tudun Wada, Karu, wanda ya jawo mutuwar dabbobin makiyayan.
"Makiyayan sun kwace bindigar janar din domin kare kansu sannan suka kai rahoto ga ‘yan sanda."

An bukaci a sako shugaban Miyetti Allah

Waziri ya ce shugaban Miyetti Allah bai da hannu a rikicin da ya faru, amma ya shiga tsakani domin kawo sasanci kan abin da ya faru.

“An kama shi duk da cewa ba shi da hannu a lamarin, laifinsa kawai shi ne kokarin shiga tsakani da ya yi domin ganin an yiwa kowane bangare adalci..”

Ya ce kokarin ganin Bello Bodejo ya ci tura, yayin da sojojin suka hana lauyoyi da danginsa ganawa da shi.

Kara karanta wannan

Shugaban masu garkuwa da mutane, Idris Alhaji Jaoji ya shiga hannu

Waziri ya yi kira ga hukumomin soji da su saki Bodejo tare da gudanar da bincike na gaskiya kan lamarin Tudun Wada domin tabbatar da adalci.

Farkon cafke shugaban Miyetti Allah

A wani labarin, mun ruwaito cewa a ranar 23 ga watan Janairu, an kama Bello Bodejo a jihar Nasarawa saboda kaddamar da kungiyar ‘yan bangar Miyetti Allah.

Bodejo ya ce 'yan banga za su taimaka wa jami'an tsaro wajen yaki da miyagun laifuka a jihar Nasarawa, amma gwamnati ta zarge shi da hada kungiyar mayaka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.