'Yan Bindiga Sun Sace Mata da Yara Sama da 50 a Gari Guda? Gwamna Ya Yi Bayani
- Gwamna Dauda Lawal ya ce labarin da ke yawo cewa ƴan fashin daji sun sace mutane 50 a yankin Maradun ba gaskiya ba ne
- Dauda ya bayyana cewa har yanzun bai samu labarin wannan hari da ake cewa an yi garkuwa da mata da ƙananan yara ba
- Ya kuma jaddada matsayarsa cewa ba zai zauna teburin sulhu da ƴan bindiga ba sai dai idan su ne suka saduda, suka nemi zaman lafiya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara - Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya musanta rahoton da ake yaɗawa cewa ƴan bindiga sun sace mata da ƙananan yara a karanar hukumar Maradun.
Wasu rahotanni da ke yawo a kafafen watsa labarai sun yi ikirarin cewa ƴan bindiga sun sace mata da yara akalla 50 a kauyen Kakin Dawa.
A wata hira da Channels tv, Gwamna Lawal ya ce wannan labarin ƙarya ne domin ko mutum ɗaya ba a sace ba a kauyen ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna ga musanta sace mutum 50 a Zamfara
Gwamnan ya ce:
"Ban da masaniya, ina cikin Zamfara, ban samu labarin harin ba. Ban san cewa an yi garkuwa da mutane 50 a karamar hukumar Maradun ba, duk wanda ya faɗa maku to ƙarya yake."
Dauda ya ƙara da cewa gwamnatinsa na aiki kafaɗa da kafaɗa da rundunar ‘yan sanda, sojoji, da sauran jami’an tsaro domin magance matsalar tsaro a jihar Zamfara.
Ya ce haɗin guiwar gwamnatinsa da jami'an tsaro ya fara haifar da sakamako mai kyau domin garkuwa da mutane ya ragu matuƙa.
Gwamnatin jihar Zamfara na nan kan bakarta
Da aka tambaye shi ko gwamnatinsa za ta duba yiwuwar tattaunawa da ‘yan bindiga, gwamnan ya yi fatali da batun nan take.
Gwamna Dauda Lawal ya ce gwamnatinsa ba ta shiga wata tattaunar sulhu domin samun zaman lafiya da ƴan ta'adda ba kuma ba ta da niyyar hakan.
"Ba zan shiga tattaunawar neman sulhu da waɗannan mutanen ba, ba zan nemi sulhu da ƴan bindiga ba, ko da zan yarda mu tattauna to sai dai idan ni ne a sama," in ji shi.
Sojoji sun ragargaji ƴan bindiga a Zamfara
Rahoto ya zo cewa sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro, sun samu nasara kan ƴan ta'adda a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma
Jami'an tsaron sun kai samame kan maɓoyar ƴan ta'adda inda suka hallaka da dama daga cikinsu a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng