Majalisar Dattawa Ta Amince da Kudurin Kafa Sabuwar Jami'ar Tarayya a Arewa
Abuja - Majalisar dattawa ta amince da kudurin kafa sabuwar jami'ar hakar ma'adanai ta tarayya a jihar Filato da ke Arewacin Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Majalisar ta amice da wannan kuduri ne a zamanta na yau Talata, 10 ga watan Disambar 2024 a Abuja.
Rahoton NTA News ya nuna cewa majalisar dattawan ta amince da kudurin kafa jami'ar ma'adanai ta tarayyar a garin Jos, babban birnin Filato.
A shekarar da ta gabata ne shugaban kwamitin kwadago da daukar aiki na majalisar dattawa, Sanata Diket Plang ya gabatar da bukatar samar da jami'ar ma'adanan.
Sanata Plang, ya jaddada bukatar soke dokar da ta kafa Cibiyar ma’adanai da kimiyyar kasa ta Najeriya domin share fagen kafa jami’ar ma’adanai da kimiyyar kasa ta tarayya a Jos.
Dan majalisa mai wakiltar Filato ta tsakiyar, ya bayyana cewa ba za a iya misalta muhimmancin da masana'antun hakar ma'adinai ke da shi a Najeriya ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa kafa jami'ar ma'adanai a Filato zai taimakawa gwamnati na cimma burinta na neman habaka tattalin arzikinta, inji rahoton Tribune.
Cikakken labarin na zuwa...
Asali: Legit.ng