Dattawa Sun Yanke Shawara, Sun Fadawa Tinubu Sabuwar Jihar da Suke So a Kirkira

Dattawa Sun Yanke Shawara, Sun Fadawa Tinubu Sabuwar Jihar da Suke So a Kirkira

  • Dattawan Igbo sun nuna goyon baya ga kafa jihar Anioma, suna masu kira ga shugaba Bola Tinubu da ya biya masu bukatarsu
  • Majalisar UNIEC ta ce kafa jihar Anioma zai tabbatar da daidaito da kuma bunkasar tattalin arziki a shiyyar Kudu maso Gabas
  • Dattawan sun yi ikirarin cewa an dade ana nuna wariya ga kabilar Igbo a siyasar Najeriya, don haka dole a kafa jihar Anioma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kudancin Najeriya - Kungiyar majalisar dattawan Igbo (UNIEC) ta tabbatar da goyon bayanta ga kafa jihar Anioma, inda ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya dauki mataki a kai.

Dattawan sun jaddada bukatar kafa sabuwar jihar a cikin wata sanarwa mai taken, “majalisar dattawan Igbo na ci gaba da fafutukar kafa jihar Anioma."

Kara karanta wannan

Tsohon mai ba Jonathan shawara ya fadi abin da zai faru da tattalin Najeriya kwanan nan

Dattawan Igbo sun yi magana yayin da suke fafutukar kafa jihar Anioma a Kudu maso Gabas
Dattawan Igbo sun bukaci Shugaba Tinubu ya goyi bayan samar da jihar Anioma. Hoto: @officialABAT, @Hope_Uzodimma1
Asali: Twitter

Igbo na so a kirkiri jihar Anioma

Sanarwar, da Justis Alpha Ikpeama da Farfesa Obasi Igwe suka sanyawa hannu, ta bayyana bukatar ba da fifiko ga kafa jihar Anioma, a cewar rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar UNIEC ta ce:

“Ba mu adawa da kafa jihohi irinsu Aba, Adada, Etiti, Njaba, Orashi, Orlu, ko wasu a Kudu maso Gabas."

Amma ta jaddada cewa, “muna matukar goyon bayan cewa jihar Anioma ta samu fifiko fiye da sauran jihohin da ake so a kirkira.”

Dattawa sun aika sako ga shugaba Tinubu

Majalisar ta kara da cewa an dade ana mayar da al’ummar Igbo saniyar ware a tsarin siyasar Najeriya, don haka kafa jihar Anioma ya zama wajibi yanzu.

“Muna kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya saurari kiraye-kirayen jama’ar Anioma da al’ummar Igbo don kafa jihar Anioma,”

- UNIEC.

Dattawan sun ce kafa sabuwar jihar Anioma zai kawo ci gaba a yankin, tare da taimaka wa Najeriya baki daya ta fuskar ci gaban tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Shugaban masu garkuwa da mutane, Idris Alhaji Jaoji ya shiga hannu

Sanata ya bukaci krikirar jiha a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa sanata Kawu Sumaila ya gabatar da kudiri a majalisar tarayya na neman kirkirar sabuwar jiha a Kano.

Kudurin wanda a halin yanzu ya tsallake karatu na farko, na nufin kirkirar sabuwar jiha mai suna 'Jihar Tiga' kuma za a cire ta daga jihar Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.