Shehu Sani Ya Yi Kaca Kaca da Zancen Sanusi II na Kiran Mace ta Mari Mijinta
- Sanata Shehu Sani ya soki kiran sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, na cewa mata su rama duka idan mazajensu sun mare su
- Shehu Sani ya yi kira ga ma’aurata su kauce wa tashin hankali a gidajensu, su kuma koyi zaman hakuri da juna
- Legit ta tattauna da wata dattijuwa a jihar Gombe mai suna Aisha Muhammad domin ba matan aure shawara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Sanata Shehu Sani ya caccaki furucin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II na cewa mata su rama duka idan mazajensu sun mare su.
Sanatan ya bayyana cewa irin wannan shawara na iya kara janyo fitina a gidaje maimakon samar da mafita ga rikice-rikicen aure.
Shehu Sani ya wallafa a Facebook cewa ya kamata ma’aurata su rika hakuri da fahimtar juna, su kuma guji tashin hankali a gidajensu domin kaucewa mutuwar aure.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kiran Sanata Shehu Sani ga ma’aurata
Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa maimakon dukan juna, ya fi dacewa ma’aurata su rika magance fushinsu lokacin da matsaloli suka taso.
Ya shawarci maza su fita daga gida idan suna cikin fushi, yayin da mata su koyi yin shiru idan mazajensu suna cikin tashin hankali har zuwa lokacin da za su natsu.
Illar rama duka tsakanin ma’aurata
Sanatan ya bayyana cewa duk lokacin da mace ta rama mari daga mijinta, hakan na iya kawo karshen zaman aure ko da kuwa sun cigaba da zama tare.
Ya ce irin wannan hali yana kara yawan rabuwar aure, wanda ke haifar da mace ta shiga rayuwar da ba ta dace ba, musamman ma a Arewacin Najeriya.
Muhimmancin hakuri da juriya a aure
Shehu Sani ya yi kira ga ma’aurata su fahimci cewa aure yana da kalubale, kuma hakuri da juna ne zai ba da damar shawo kan matsalolinsa.
Ya kara da cewa aure ba na wadanda ba sa kuskure ba ne, amma idan ma’aurata suka koyi yadda za su jure zaman tare, za su iya tsallake kowace irin matsala.
Legit ta tattauna da Aisha Muhammad
Wata dattijuwa a jihar Gombe, Aisha Muhammad ta ce bai kamata mace ta daga hannu ta mari mijinta ba.
Aisha ta ce idan aka samu sabani, mace ta kai kara wajen na gaba da su idan ba za ta iya hakuri ba maimakon cewa za ta yi fada da mijinta.
Muhammadu Sanusi II ya gargadi iyaye kan tarbiyya
A wani rahoton, kun ji cewa sarki Muhammadu Sanusi II ya ja hankalin iyaye kan kula da tarbiyar 'ya'yansu domin samar da al’umma ta gari.
Muhammadu Sanusi II ya bayyana haka ne yayin da hakimai da shugabannin kananan hukumomi da suka ziyarce shi a fadar Sarkin Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng