Tattalin Arziki: Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Yadda Za a Samu Sauki a Shekarar 2025

Tattalin Arziki: Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Yadda Za a Samu Sauki a Shekarar 2025

  • Ministan tattalin arziki da kudi, Wale Edun, ya bayyana cewa tattalin Najeriya zai samu ingantuwa a shekara mai zuwa
  • Wale Edun ya bayyana cewa karin kudin shiga zai rage yawan basussuka da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa
  • Haka zalika ministan ya bayyana cewa kasafin kudin 2025 zai samar da ci gaba mai dorewa da amfani ga 'yan kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ministan kudi na kasa, Wale Edun, ya bayyana cewa akwai tabbacin cewa tattalin arzikin Najeriya zai inganta sosai a shekara mai zuwa.

Ministan ya fadi haka ne a wani taron kwamitocin majalisar wakilai kan tsare-tsaren tattalin arziki da kasafin kudin shekarar 2025 da aka kiyasta zai kai Naira tiriliyan 47.9.

Wale Edun
Gwamnati ta ce za a samu sauki a 2025. Hoto: Bayo Onanuga|Wale Edun
Asali: Twitter

The Nation ta wallafa cewa Wale Edun ya yi bayanin cewa Najeriya tana farfadowa daga matsalolin tattalin arziki da suka dade suna shafar kasa da rayuwar jama’a.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun rikita gari da harbi, sun bi gida gida sun dauki mata da yara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, tsare-tsaren da ake gudanarwa a halin yanzu suna nuna kyakkyawar alamar ci gaba a nan gaba.

Bayani a kan kasafin kudin 2025

A yayin da yake bayani kan kasafin kudin shekara mai zuwa, Ministan ya nuna cewa ana sa ran karin kudin shiga, wanda hakan zai rage dogaro da karbar bashi daga kasashen waje.

Ministan ya ce karin kudin zai taimaka wajen biyan basussuka da kuma samar da wani yanayi mai dorewa ga tattalin arzikin kasa.

Tribune ta wallafa cewa Wale Edun ya ce an tsara kasafin kudin 2025 ne domin samar da ci gaba wanda zai amfani kowa da kowa a Najeriya.

Shirin gwamnatin Tinubu a shekarar 2025

Ministan ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tana daukar matakai na gyara tsare-tsaren tattalin arziki domin samar da yanayi da zai karfafa saka hannun jari.

Hakan na nufin cewa za a samu ci gaba mai dorewa wanda zai inganta rayuwar al’umma gaba daya.

Kara karanta wannan

Gyaran haraji: Hanyoyi 20 da talakawa, ƴan kasuwa za su amfana da kudurin Tinubu

Ministan ya ce hakan na cikin burin gwamnatin Najeriya na tabbatar da samun ci gaba mai amfani da kuma dorewa ga dukkan al’ummar kasa.

CBN ya yi magana kan matsalar tattali

A wani rahoton, kun ji cewa bankin CBN ya tabbatar da cewa har yanzu Najeriya na fama da matsalar tattalin arziki.

Gwamnan CBN ya bayyana cewa ma'aikatan banki na da matuƙar muhimmanci wajen magance kalubalen tattali da Najeriya ke fuskanta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng