Tinubu Ya Gamu da Gagarumar Matsala, Hukuma Ta Ki Amincewa da Gyaran Haraji

Tinubu Ya Gamu da Gagarumar Matsala, Hukuma Ta Ki Amincewa da Gyaran Haraji

  • Hukumar RMAFC ta ce dokokin gyaran haraji sun sabawa kundin tsarin mulki saboda sun takaita huruminta wajen tsara rabon kudi
  • RMAFC ta ba gwamnatin tarayya shawarar amfani da tsarin rabon VAT na hukumar domin tabbatar da adalci ga bangarorin gwamnati
  • Hukumar ta gargadi gwamnati cewa dokokin za su iya zama barazana ga hadin kan kasa tare da haifar da rashin fahimta a rabon kudi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar RMAFC ta nuna adawa da dokokin gyaran haraji na shugaba Bola Tinubu, tana mai zargin sun sabawa kundin tsarin mulki.

A wata takarda mai shafuka tara da RMAFC ta fitar, hukumar ta bayyana kura kuran kudurorin harajin da suka shafi doka da tsarin mulki.

Hukumar RMAFC ta yi magana yayin da dokar gyaran haraji ke gaban majalisar tarayya
Hukumar RMAFC ta fadawa Tinubu kuskuren da ya yi a dokar gyaran haraji. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Hukumar RMAFC na adawa da gyaran haraji

Shugaban RMAFC, Mohammed Bello Shehu, ya ce kundin tsarin mulki na 1999 ya bai wa hukumar damar tsara tsarin rabon kudaden gwamnati, inji rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

'Ku kwantar da hankalinku': Sultan kan kudirin haraji bayan ganawa da Ribadu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mohammed Shehu ya jaddada cewa RMAFC ita ce kadai hukumar da ke da hurumin tsara tsarin raba kudaden cikin adalci da gaskiya.

“Dokar kundin tsarin mulki ta bayyana RMAFC a matsayin hukumta ta karshe kan sha’anin rabon kudade,” in ji takardar.

RMAFC na so Tinubu ya mutunta huruminta

Hukumar ta ce duk wani yunkuri na aiwatar da dokar gyaran haraji ko wata dokar da za ta takura aikinta ya saba wa tsarin mulki.

The Cable ta rahoto RMAFC ta jaddada muhimmancin mutunta huruminta wajen tabbatar da rabon kudade cikin adalci da gaskiya.

Hukumar ta bada shawarar amfani da tsarin da ta tsara wajen raba kudin harajin VAT domin tabbatar da rabon da ya dace ga bangarorin gwamnati.

Gyaran haraji: RMAFC ta gargadi Tinubu

Takardar ta bukaci shugaba Bola Tinubu da ya ba da dama ga hukumar RMAFC ta kammala tsarin raba VAT bisa kundin tsarin mulki kafin aiwatar da gyaran haraji.

Kara karanta wannan

'Yan kasuwa sun tafka asara, wuta ta babbake miliyoyin Naira a Nasarawa

RMAFC ta ce dole ne a samu fahimta tsakanin gwamnoni da bangarorin gwamnati don tabbatar da karbar tsarin cikin lumana.

Hukumar ta gargadi cewa dokokin za su iya kawo baraka ga hadin kan kasa, tare da jaddada muhimmancin adalci da gaskiya a rabon kudade.

Amfanin gyaran haraji ga talaka da 'yan kasuwa

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ba 'yan Najeriya tabbacin cewa gyaran haraji zai zamo mai amfani da ga talaka da kananun 'yan kasuwa.

A wata sanarwa da shugaban kwamitin shugaban kasa kan gyaran haraji ya fitar, ya lissafa hanyoyi 20 da gyaran haraji zai amfani talakawan kasar da kananun 'yan kasuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.