Gwamna Ya Faɗi Dalilin da Ya Sa Mahaifinsa Ya Auri Mata sama da 30 a Rayuwarsa
- Gwamnan Ebonyi ya taɓo rayuwar mahaifinsa, ya faɗi dalilin da ya sa ya auri mata sama da 30 kuma ya tara ƴaƴa sama da 100
- Francis Nwifuri ya bayyana cewa mahaifinsa ya fuskanci tsana, tsangwama da wulakanci saboda arzikin da Allah ya ba shi dare ɗaya
- Gwamna Nwifuri ya faɗi haka ne a wurin bikin naɗa mahifainsa sarauta a sabuwar masarautar da majalisa ta kirkiro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ebonyi - Gwamna Francis Nwifuru na Ebonyi ya bayyana dalilin da yasa mahaifinsa, Ezekiel Nwifuru ya auri mata sama da 30 kuma ya tara ‘ya’ya 108.
Nwifuru ya taɓo rayuwar mahaifinsa ne a wurin biki naɗa shi sarautar sarkin sabuwar masarautar Oferekpe Agbaja da aka kirkiro a jihar Ebonyi.
Yadda mahaifin gwamna ya auri mata fiye da 30
Premium Times ta ce a farko mahaifin gwamnan ya auri mata sama da 30, amma ya rage su zuwa 19 bayan rabuwa da wasu matan saboda rashin haihuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin mata 19 da suka haifi ‘ya’ya 108, sabon basaraken na nan tare da matansa 17 a halin yanzu.
Majalisar dokokin jihar Ebonyi ce ta kirkiro dokar kafa masarautar Oferekpe Agbaja wanda ta ƙunshi kauyuka 17, an cire ta daga yankin Agbaja.
Dalilin da mahaifin gwamnan ya auri mata 30
Da yake jawabi, Gwamna Nwifuru ya ce mahaifinsa mai shekaru 84 ya zama mai arziki dare ɗaya ta hanyar aiki tukuru a matsayinsa na manomi.
Ya ce arzikin da Allah ya yi babansa lokaci ɗaya ya jawo masa hassada, tsana, tsangwama, barazana da cin mutunci kala-kala daga ƴan uwansa a Agbaja.
Gwamnan ya ce mahaifinsa mutum ne mai himma wanda ‘yan uwa, makwabta, da sauran al’umma suka wulakanta shi saboda nasarar da ya samu, The Sun ta rahoto hakan.
Ya ce tsanar da aka riƙa nuna masa da wulakanci ne ya sa mahaifinsa ya auri mata da yawa a matsayin abokan zama kuma hakan ya taimaka wajen cimma burinsa.
"Mahaifina ya auri mata da yawa ne saboda cin mutunci da wulaƙancin da mutanen kauye suka masa sabida ɗaukakar da Allah ya ba shi," in ji Nwifuru.
Gwamna Nwifuru ya ƙara dakatar da kwamishina
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Francis Nwifuru ya sake dakatar kwamishina daga aiki saboda wasa da aiki da sakaci.
Ya zuwa yanzu dai gwamnan ya dakatar da kwamishinoni guda huɗu bayan ya zarge su da aikata laifuffuka daban-daban.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng