Gyaran Haraji: Hanyoyi 20 da Talakawa, Ƴan Kasuwa Za Su Amfana da Kudurin Tinubu

Gyaran Haraji: Hanyoyi 20 da Talakawa, Ƴan Kasuwa Za Su Amfana da Kudurin Tinubu

  • Taiwo Oyedele, jami'in gwamnatin tarayya ya bayyana yadda talakawa da kananan 'yan kasuwa za su amfana da gyaran haraji
  • Ya sanar da cewa sababbin dokokin haraji sun kawo bukatar cire VAT a kan sufuri, abinci, ilimi da kariya ga masu karamin albashi
  • Rangwamen haraji zai taimaka wa talakawa da 'yan kasuwa domin samar da yanayi mai kyau na kasuwanci da bunkasarsa a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban kwamitin shugaban kasa kan sauye-sauyen haraji, Taiwo Oyedele, ya bayyana hanyoyin da gyaran haraji zai amfanar da 'yan Najeriya.

A wata sanarwa a ranar Litinin, 9 ga Disamba, Oyedele ya bayyana yadda talakawa da kananan 'yan kasuwa za su amfana daga wannan sauye-sauyen.

Shugaban kwamitin shugaban kasa ya yi magana kan amfanin gyaran haraji
Taiwo Oyedele ya bayyana amfani 20 da gyaran haraji ke da shi ga talaka da 'yan kasuwa. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

A cewar Oyedele a shafinsa na X, babu wani bangare da sababbin dokokin harajin bai taba ba, kuma amfaninsa ya fi rashin amfaninsa yawa.

Kara karanta wannan

Matasan N-Power na jiran bashinsu, gobara ta laƙume ma'ajiyar NSIPA, kaya sun kone

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hanyoyin da za ku amfana da sauye-sauyen haraji:

Amfanin gyaran haraji ga talakawa

  1. An cire harajin PAYE gaba daya ga masu samun albashi na kasa da N1m a shekara (kimanin N83,000 a wata).
  2. An rage harajin PAYE ga masu albashi na kasa da N1.7m a wata.
  3. An cire harajin VAT (ya koma 0%) a kan abinci, kiwon lafiya, ilimi, samar da wutar lantarki da watsa ta.
  4. An cire VAT a kan sufuri, makamashi, CNG, kayan jarirai, audugar al'ada, kudin haya da kayayyakin mai.
  5. An sanya haraji mai rangwame ga tallafin sufuri da karin albashi ga masu karamin karfi.
  6. Rangwamen haraji ga masu daukar sababbin ma'aikata sama da wadanda suka dauka cikin shekaru 3 da suka gabata.
  7. An cire harajin hatimi a kan kudin hayar kasa da N10m.
  8. Harajin PAYE bai shafi sauran jami'an tsaro da ke yaki da rashin tsaro ba.
  9. Dokoki masu sassauci ga ma’aikatan da ke aiki daga gida da masu ayyukan intanet.
  10. Karin haske kan harajin kadarorin intanet don gujewa biyan haraji sau biyu da bayar da damar rage hasara.

Kara karanta wannan

TCN zai magance matsalolin wutar lantarki, an fara inganta manyan tashoshi 3

Amfanin gyaran haraji ga kananan 'yan asuwa

  1. An kara yawan kudin kasuwanci da ake cirewa haraji daga N25m zuwa N50m a shekara.
  2. An cire harajin kuɗin kamfani ga kananan 'yan kasuwa (harajin ya koma 0%).
  3. Babu haraji kan kuɗin shigar kananan 'yan kasuwa.
  4. Ba za a cirewa kananan 'yan kasuwa haraji daga kudaden biyan masu kaya ba.
  5. Saukaka yin bayani kan asusun kasuwanci ta hanyar amfani da bayanan mai kasuwanci maimakon takardun bincike na kudi.
  6. Kafa ofishin kare masu biyan haraji don kare su daga kin adalcin gwamnati wajen tara haraji.
  7. Magance takaddamar haraji tsakanin gwamnati da 'yan kasuwa a cikin kwanaki 14.
  8. Dunkule haraji waje daya da kuma janye harajin da aka maimaita.
  9. Haramta karɓar kuɗi ta hanyar da ke kuntatawa 'yan kasuwa.
  10. Samar da tsarin haraji mai jan hankali domin ba 'yan kasuwa damar zamantar da kasuwancinsu da kuma habaka su.

Amfanin gyaran haraji ga yankin Arewa

Kara karanta wannan

Bayan shawarar Kwankwaso, Jibrin Kofa ya nemi afuwa kan goyon bayan kudirin haraji

A wani labarin, mun ruwaito cewa Daniel Bwala, mai ba wa shugaban kasa shawara kan harkokin sadarwa, ya bayyana cewa dokokin gyaran haraji za su amfani talakawan yankin Arewa.

Ya ce sabanin ra'ayin da wasu ke da shi, sabbin dokokin harajin ba za su kara talauta yankin Arewa ba, inda mutane da dama daga yankin ke maraba da gyaran.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.