'A Kyale Talaka': Farfesa a Kano Ya Fadawa Tinubu Mutanen da Zai Karawa Haraji

'A Kyale Talaka': Farfesa a Kano Ya Fadawa Tinubu Mutanen da Zai Karawa Haraji

  • Farfesa Kabiru Dandago ya bukaci gwamnati da ta kara haraji kan kadarori da kayayyakin alatu, ba tare da kara harajin VAT ba
  • Ya ce haraji kan kadarori, alatu zai nunka kudaden shiga, tare da rage gibin da ke tsakanin talakawa da masu hannu da shuni
  • Farfesan ya yi gargadi kan harajin "kudin shigar iyalai," wanda zai iya zama wata hanya ta haraji kan gado ko kyaututtuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Farfesa Kabiru Dandago na jami’ar Bayero, Kano ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara haraji kan masu arziki, maimakon kara harajin VAT.

Malamin jami'ar ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya saka haraji kan kadarori, kayayyakin alatu da hada hadar manyan kudi domin samun karin kudin shiga.

Farfesa Kabiru Dandago ya yi magana kan harajin VAT da ake son karawa
Farfesa Dandago ya bukaci Tinubu ya hakura da harajin VAT, ya karawa masu kudi harajin. Hoto: @officialABAT
Asali: Facebook

Farfesa ya bukaci Tinubu ya gyara haraji

Kara karanta wannan

Gyaran haraji: Hanyoyi 20 da talakawa, ƴan kasuwa za su amfana da kudurin Tinubu

A wata hira da jaridar Daily Trust, Farfesa Dandago ya ce harajin kadarori, kayan alfarma da hada hadar manyan kudi za su ninka kudaden da ake samu daga VAT.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesan ya ce wannan mataki zai taimaka wajen rage gibin arziki tsakanin masu kudi da talakawa, ta hanyar kara nauyin haraji kan masu hannu da shuni.

Ya bayar da misali cewa haraji kan hada hadar manyan kudi zai shafi masu kudin da ke kasuwancin sama da Nira miliyan goma ne.

Farfesa ya yi gargadi kan harajin gado

Dandago ya nuna damuwa kan wani haraji da aka kira "family income tax" wanda ya ke nufin kakaba haraji kan gado ko ba da wani abu kyauta.

Ya ce harajin zai iya zama kamar na "biri da shan duka gardi da karbar kudi," inda gwamnati za ta rika karbe kason dukiyar gado ko ta kyaututtuka.

A bangaren siyasa, Baba Yusuf ya ce yana ganin gwamnoni sun ki amincewa da kudirin harajin ne kawai don bukatunsu ba na jama’a ba.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna a Arewa ya saba da 'yan yankin, ya soki masu caccakar kudirin haraji

Haraji: Jigon PDP ya gano kuskuren Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Segun Sowunmi, wani jigon jam'iyyar PDP ya ce shugaba Bola Tinubu ne ya jawo 'yan Najeriya ke adawa da kudurin gyaran haraji.

Segun Sowunmi ya bayyana cewa kuskuren da Shugaba Tinubu ya yi shi ne mayar da shugabannin Arewa saniyar ware yayin shirya kudirin harajin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.