'Yan Kasuwa Sun Fara Dakon Fetur Kai Tsaye daga Matatar Ɗangote

'Yan Kasuwa Sun Fara Dakon Fetur Kai Tsaye daga Matatar Ɗangote

  • Kungiyar dillalan man fetur ta ƙasa (IPMAN) ta tabbatar da fara dakon fetur daga matatar Ɗangote
  • Lamarin ya tabbata ne a watan Nuwamba, inda IPMAN ta ce an fara sayar mata da fetur ta kamfanin MRS Oil
  • Wannan na zuwa bayan kamfanin da matatar sun sha zama domin sahale mata dakon fetur kai tsaye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Kungiyar dillalan man fetur ta ƙasa (IPMAN), ta fara dakon man fetur kai tsaye daga matatar mai ta Ɗangote da ke Legas.

Lamarin ya tabbata ne bayan kungiyar ta sha tattauna wa da matatar domin ba ta damar sayo fetur kai tsaye.

Fetur
IPMAN ta fara dakon fetur daga Ɗangote Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

Jaridar Punch ta wallafa cewa sakataren yaɗa labaran IPMAN, Chinedu Ukadike ya tabbatar da cewa sun fara ɗauko fetur kai tsaye daga matatar Dangote.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai harin ban mamaki, sun kashe wata ƴar Kasuwa da malamin addini

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗangote: Yaushe IPMAN ta fara dakon fetur?

Legit.ng ta ruwaito cewa ƙungiyar IPMAN ta tabbatar da fara dakon fetur daga matatar Ɗangote a watan Nuwamba, 2024.

Sakataren yaɗa labaran ƙungiyar, Chinedu Ukadike ya ce a halin da ake ciki, ƴan kasuwar su na dakon fetur ta kamfanin MRS Oil.

Ukadike ya ce;

“Mun yi wani tsari tun farko. Kwararrunmu su na harhaɗa takardunmu. Kamfanin Dangote Refinery ya samar mana da wasu kayayyaki ta MRS, kuma mun fara lodawa a hankali (a watan Nuwamba). Muna sayen fetur ɗin Dangote ta hannun MRS."

Farashin da IPMAN ke dakon fetur

Ƙungiyar IPMAN ta sanar da fara dakon fetur daga matatar Ɗangote da ke Legas a ƙasa da N1,0000 a kan kowace lita.

Ukadike ya ce ragin farashin litar fetur da matatar Ɗangote ta yi daga N990 zuwa N970 ya jawo ƙarin bukatarsa a kasuwar cikin gida.

Ya kara da cewa yarjejeniyar da aka kulla tsakanin IPMAN da Dangote ta taimaka wajen rage farashin fetur, musamman saboda ta kawar dillalai a tsakiya.

Kara karanta wannan

2027: Bayan fara kiran Jonathan ya gwabza da Tinubu, jam'iyyar APC ta yi martani

An samu sauƙin fetur a Ɗangote

A baya mun wallafa cewa matatar mai ta Ɗangote ta cimma matsaya da ƙungiyar dillalan man fetur (IPMAN), don fara jigilar fetur kai tsaye daga matatar zuwa gidajen mansu.

Shugaban ƙungiyar IPMAN na ƙasa, Abubakar Garima ne ya tabbatar da haka, tare da miƙa buƙatar dillalan man fetur su mara wa matatar Ɗangote baya domin akwai alheri a yarjejeniyar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.