Sojoji Sun Gwabza Kazamin Fada da 'Yan Bindiga, An Kwato Motar 'Yan Ta'adda

Sojoji Sun Gwabza Kazamin Fada da 'Yan Bindiga, An Kwato Motar 'Yan Ta'adda

  • Sojojin Najeriya karkashin Operation Whirl Stroke sun kaddamar da farmaki mai suna "Operation Golden Peace" a Taraba da Benue
  • Sojojin sun yi nasarar fatattakar ‘yan bindiga a wasu yankuna na karamar hukumar Ukum, tare da kwato wasu kayayyaki
  • Shugaban rundunar, Birgediya Janar Kingsley Uwa, ya yaba da jarumtar sojojin tare da cewa za su cigaba da kokari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue - A ci gaba da kokarin dawo da zaman lafiya a yankunan Taraba da Benue, rundunar sojojin Najeriya ta kaddamar da farmaki da ta rada wa suna "Operation Golden Peace."

Farmakin ya mayar da hankali ne kan fatattakar ‘yan bindiga da suka addabi yankunan Akahagu da China a karamar hukumar Ukum ta jihar Benue.

Kara karanta wannan

Sojoji, 'yan sanda da 'yan banga sun hadu sun gwabza da tulin 'yan bindiga

Sojoji
Sojoji sun fatattaki 'yan ta'adda a Benue. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Rundunar sojin ta wallafa a Facebook cewa sojojin sun samu nasara ta hanyar lalata sansanonin ‘yan bindiga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farmakin sojoji kan sansanin ‘yan bindiga

Rahoton VON ya nuna cewa a ranar 7 ga Disamba, 2024, sojoji suka kaddamar da farmaki a garuruwan Akahagu da China na jihar Benue.

Haka kuma, farmakin ya shafi yankin Ikayor, inda suka fafata da ‘yan bindiga da ke da alaka da wani dan ta’adda mai suna Akiki Utiv, wanda aka fi sani da "Full Fire."

Sojoji sun kwato motar 'yan ta'adda

Bayan musayar wuta mai tsanani, sojojin sun samu nasarar tarwatsa ‘yan bindigar, wadanda suka tsere bayan sojoji sun nuna musu karfin makamai.

Daga cikin kayayyakin da aka kwato akwai wata mota kirar Toyota Corolla, babur, wandon sojoji da bindiga kirar Beretta.

Dakarun Sojoji sun yi kira ga al'umma

Shugaban rundunar sojojin runduna ta 6, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya jinjinawa jarumtar sojojin da suka kai farmaki.

Kara karanta wannan

Shugaban masu garkuwa da mutane, Idris Alhaji Jaoji ya shiga hannu

Birgediya Janar Kingsley ya bayyana cewa nasarar ta nuna kokarin sojoji na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihohin Taraba da Benue.

Ya yi kira ga al’ummar yankunan da su kasance masu hadin kai tare da bayar da bayanai masu amfani ga jami’an tsaro domin samun nasarar kakkabe duk wani nau’i na ta’addanci.

Sojoji za su murkushe Lakurawa

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya tare da da wasu ƙasashe makwabta sun fara sintiri a iyakoki domin murkushe Lakurawa.

Wasu masana sun bayyana damuwa kan yadda iyakokin Najeriya suke ba da damar karuwar rashin tsaro a Arewa ta Yamma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng