Rarara: Fitaccen Mawakin Siyasa a Arewa Zai Gina Masallacin N350m a Mahaifarsa

Rarara: Fitaccen Mawakin Siyasa a Arewa Zai Gina Masallacin N350m a Mahaifarsa

  • Fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya tattago babban aikin alkairi na gina babban masallacin Juma'a a mahaifarsa
  • An rahoto cewa masallacin da mawaki Rarara zai gina a Kahutu da ke Danja, jihar Katsina zai lakume kusan Naira miliyan 350
  • Gina masallacin na daga cikin ayyukan raya kasa da mawaki Rarara ke yi a Arewacin kasar, inda ya yi makamancin hakan a Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Fitaccen wawakin siyasar Arewa, Dauda Kahutu Rarara ya kaddamar da ginin babban masallacin Juma’a a garin Kahutu.

Kahutu, wani gari ne da ke a cikin karamar hukumar Danja, jihar Katsina, inda nan ne mahaifar mawaki Rarara.

Fitaccen mawakin siyasa, Rarara zai gina katafaren masallacin juma'a a mahaifarsa
Mawaki Rarara ya kaddamar da gina katafaren masallacin juma'a a mahaifarsa. Hoto: Rabi'u Garba Gaya
Asali: Facebook

Mawaki Rarara zai gina masallacin N350m

Rahoton shafin Kannywood Empire ya nuna cewa Dauda Kahutu Rarara zai kashe kimanin Naira miliyan 350 wajen gina wannan masallaci.

Kara karanta wannan

Kudirin haraji da abubuwa 9 da suka yi wa gwamnatin Tinubu illa a Arewacin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ginin wannan masallacin ya kara nuna ci gaba a ayyukan alheri da Mawaki Rarara ya saba gudanarwa a yankuna daban-daban.

Mutanen garin Kahutu sun bayyana farin ciki da godiya ga wannan gagarumin aiki da Rarara ya kaddamar masu, tare da addu'ar Allah ya bashi ikon kammalawa.

Ayyukan alherin mawaki Rarara a Arewa

Wani furodusa a Kannywood, Hamza Lawan Abubakar ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa Rarara ya fara gina masallaci a Kuderi da ke Sumaila, jihar Kano, a makon jiya.

Furodusa Hamza Dandago, ya ce mawaki Rarara ya kuma ya gina makarantu da azuzuwa domin bunkasa karatun firamare a karkara da birane.

"Hakazalika, ya gina rijiyoyin burtsatse a kauyuka daban-daban domin taimakawa al’ummomin karkara samun ruwan sha mai tsafta."

- A cewar mai shirya fina finan.

Kano: Rarara ya kaddamar da ginin titi

A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen mawakin siyasa a Arewa, Dauda Kahutu Rarara ya amsa koken mazauna yankin Darmanawa a jihar Kano, na gina masu titi.

Mai magana da yawun Rarara, Rabi'u Garba Gaya ya ce mawakin ya ba da umarnin fara aikin titin daga ofishin yan sanda na Darmanawa zuwa Gandun Sarki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.