Sokoto: Jigon PDP Ya Dauki Nauyin Kaciyar Yara 1,000, An Kwarara Masa Yabo
- Yayin da aka shiga lokacin hunturu musamman a Arewacin Najeriya, jigon PDP ya taimakawa iyayen yara marasa karfi
- Jigon jam'iyyar mai adawa a jihar, Faruku Fada ya dauki nauyin yara har guda 1,000 domin yi musu kaciya kyauta a jihar
- Legit Hausa ta tattauna da mai fashin baki a Sokoto mai suna Kwamred Surajo Umar Sa'adu kan abin da jigon PDP ya yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Sokoto - Wani jigo a jam’iyyar PDP, Faruku Fada ya kaddamar da shirin daukar nauyin aikin kaciya na shekara-shekara ga yara maza.
Dan siyasar ya kaddamar da shirin ne a kananan hukumomin Kudu da Arewa a jihar, inda ake sa ran yara maza akalla 1,000 za su ci gajiyar shirin a bana.
Shugaban PDP ya yabawa Faruku Fada
Punch ta ruwaito cewa kaciya na daga cikin al'adar Hausawa da ake yiwa yara kasa da shekaru 10 a lokacin hunturu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake magana a wurin taron, shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Bello Goronyo, ya yabawa Fada saboda wannan gagarumin mataki da ya dauka.
Goronyo ya ce hakan na daga cikin kokarin farfado da tsohuwar al’adar Hausawa ta iyaye da kakanni.
Jigon PDP ya yiwa yara kaciya a Sokoto
Shugaban PDP ya yi kira ga sauran masu hannu da shuni da kungiyoyi da su yi koyi da Fada wajen taimakawa al’umma.
A bangarensa, Fada ya bayyana cewa manufar shirin ita ce taimakawa iyaye marasa karfi wadanda ba za su iya daukar nauyin yi wa ‘ya’yansu kaciya ba.
Mutane da dama sun yabawa attajirin kan irin wannan kokari da kuma raya al'adun Hausawa da ya yi.
Legit Hausa ta tattauna da mai fashin baki
Kwamred Surajo Umar Sa'adu da ke Sokoto ya yabawa jigon PDP kan wanna taimako da ya yi ga al'umma.
Surajo ya ce a ajiye maganar siyasa ko son kai duba da halin da ake ciki wannan abin a yaba ne.
"A al'adar Malam Bahaushe musamman Basakkwace akan taran unguwa da suka isa kaciya mutum daya ya dauki nauyin yi musu kaciya har da abin da ya shafi abinci da kaji."
"Daga karshe za a yi bikin yaye yaran daga kaciya kuma mutum daya zai dauki nauyi."
- Kwamred Surajo Umar Sa'adu
Surajo ya ce a halin da ake ciki yanzu an dai na irin wannan wanna abin amma shi wannan attajiri ya yi abin a yaba.
Dan Majalisa ya dauki nauyin yiwa yara kaciya
Kun ji cewa Dan Majalisar Tarayya a jihar Kano ya sha suka bayan kaddamar da wani shiri na yi wa yara fiye da dubu daya a mazabarsa kaciya.
Mohammed Bello Shehu wanda ke wakiltar mazabar Fagge a Majalisar Wakilai ya kaddamar da shirin ne a jiya Lahadi 31 ga watan Disamba.
‘Yan siyasa sun soki shirin na dan Majalisar inda suka bayyana hakan a matsayin abin kunya a yankin.
Asali: Legit.ng