An yi bikin yiwa yara kaciya a Kano

An yi bikin yiwa yara kaciya a Kano

- Kokarin taimakawa yara marayu da kaciya kyauta ya zo da tangarda sakamakon rashin taimakon isassun magunguna da za a ba su kyauta

-Kungiyar wanzamai ta jihar Kano reshen karamar hukumar Nassarawa ta yi bikin yiwa yara marayu kaciya

An yi bikin yiwa yara kaciya a Kano
An yi bikin yiwa yara kaciya a Kano

A wani bikin yin kaciyar da aka gudanar a ranar Asabar 20 ga watan Janairu a unguwar Kawon Maigari a karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano, kungiyar Wanzamai reshen karamar hukumar ta yiwa marayu sama da 140 kaciya kyauta.

Sai dai a cewar mataimakin shugaban kungiyar na reshen karamar hukumar Nassaarawa kuma shugaban gudanar da kaciyar, Alhaji Gambo, su ba haka suka so ba, domin shirin ya zo da tangarda.

Kungiyar ta kuma yi musu alluar Tetanus da kuma rarraba musu magunguna da kuma ci gaba da kulawa da lafiyarsu har sai sun warke.

A hirarsa da 'yan jaridu shugaban kaciyar marayu, Alhaji Gambo Mai askin Baba na tsangayar Damagum, kan kudurin na su ya ce, burin kungiyar ne na yiwa yara mdai arayu kaciya a matsayin gudunmawarsu ga al’ummar jihar.

Sai dai a cewarsa aniyar ta su, ta samu tangarda sakamakon karanci da magungunan da za su rarrabawa ‘yan shayin kamar yadda suka tsara.

kungiyar dai na rarraba magungunan kashe zafi na Paracetamol, da na kashe kwayoyin cuta, da kuma yiwa yaran allurarTettanus wadanda duk a kyauta a duk lokacin da suka yi wa yaran shayi.

Kuma sun yi hakan a unguwannin Dakata da Kawaji a karamar hukumar a baya, sai dai karfinsu na samar da wadannan magunan ga yawan wandannan yara a yanzu ya ci tura, sakamakon rashin taimako daga karamar hukuma da kungiyoyi masu zaman kansu da kuma daidaikun jama’a.

Kungiyar ta yiwa yara kimanin 87 a unguwar Dakata da Kawaji, a inda ta kuma rarraba musu magunguna kyauta sai dai kungiyar karfinta ya kare, a cewarsa.

Sai dai duk wannan yunkuri na kungiyar da kuma bibiyar karamar hukumar Nassarawa kan tallafawa shirin a cewarsa, ya ci tura. Sai dai ba zasu gaza ba, duk da kokarinsu na yin arba da shugaban karamar hukumar Nassarawa wanda ya yi musu alkawari ya ci tura.

Ya kuma ci gaba da cewa, marasa galihu dai a jihar Kano na cikin mawuyacin hali musamman ma marayu, a inda yin kaciya na yin wahala ga yaran da suka kai munzali.

Kungiyar fito da tsarin cike fom da hoton yaro, da sa hannun mai kula da yaron, tare da sa hannun mai unguwa, da Dagaci da kuma shugaban wanzamai kafin a yiwa marayan kaciya.

Taron bikin yin kaciyar ya samu halartar dagacin Kawo, da kuma Hakimin Nassarawa wanda ya samu wakilcin wani na hannun damansa.

Ko yaya ku ka ga kokarin wannan kungiya? aiko da naku ra'ayin a shafinmu na Facebook a http://www.facebook.com/naijcomhausa ko kuma Tuwita a http://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel