Bayan Faransa, Gwamnatin Tinubu Ta Kulla Sabuwar Yarjejeniya da Kasar Pakistan

Bayan Faransa, Gwamnatin Tinubu Ta Kulla Sabuwar Yarjejeniya da Kasar Pakistan

  • Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta haɗa kai da Pakistan don bunƙasa noma da magance matsalolin abinci da sauyin yanayi
  • Jakadan kasar Pakistan ya yi alkawarin ba Najeriya duk wani goyon baya da take bukata domin bunƙasa fannin nomanta
  • An rahoto cewa gwamnatin Shugaba Tinubu na aiki tukuru domin magance kalubalen tsaro da ke hana cigaban noman a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin Tarayya za ta haɗa kai da kasar Pakistan domin bunƙasa noma da samar da isasshen abinci a Najeriya.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa da babbar jami’ar yada labarai ta ma’aikatar noma da samar da abinci, Umar Rashida ta fitar a ranar Lahadi.

Ministan noma, Sanata Abdullahi ya yi magana yayin da Najeriya ta kulla yarjejeniya da Pakistan
Najeriya da Pakistan sun kulla yarjejeniya kan noma. Hoto: @GovtofPakistan, @officialABAT
Asali: Twitter

Najeriya ta kulla yarjejeniya da Pakistan

Wannan haɗin gwiwa ya fito ne yayin ziyarar jakadan Pakistan, Manjo Janar Sohali Khan, ga ministan noma, Sanata Aliyu Abdullahi, a Abuja inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fadi halin da ake ciki game da jita jitar bullar annobar 'Korona'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Aliyu Abdullahi ya jaddada muhimmancin haɗin kai a fannin noma, yana mai cewa Najeriya tana buƙatar ƙarin abokan hulɗa a wannan fanni.

Ministan ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu na aiki tukuru kan magance kalubalen da suka shafi tsaro da sauyin yanayi a kasar.

Pakistan za ta ba 'yan Najeriya horo

Jakadan kasar Pakistan, Manjo Janar Sohali ya yi alkawarin bai wa Najeriya ƙwararrun masanan noma domin ba da horo a fannonin noma daban-daban a kasar.

Pakistan na cikin ƙasashe mafi ƙwarewa wajen fasahar noma, tana kuma ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da ke samar da kayan gona kamar auduga da shinkafa.

Majo Janar Sohali Khan ya ce ƙwararru daga Najeriya za su samu damar ziyartar Pakistan domin su koyi dabarun noma na zamani daga kwararrun Pakistan.

Najeriya ta shiga yarjejeniya da Faransa

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kulla yarjejeniyar hako ma'adanai da inganta harkar da gwamnatin kasar Faransa

An ce yarjejeniya ta kunshi cigaban fasahar makamashi ta hanyar inganta amfani da ma’adanai irin su tagulla kuma za a kare illar hakar ma'adanai ga muhalli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.