Mahaifin Gwamna a Najeriya Mai Mata 17 da 'Ya 'ya 108 Ya Zama Sarki

Mahaifin Gwamna a Najeriya Mai Mata 17 da 'Ya 'ya 108 Ya Zama Sarki

  • Kauyen Oferekpe ya cika da murna bayan nada mahaifin Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi sarki a yankin a jiya Asabar
  • Al'ummar yankin da ke karamar hukumar Izzi sun amince da nadin Eze Ezekiel Nwifuru Nwankpu a matsayin sarkinsu
  • Sabon basaraken ya auri mata 19 a rayuwarsa amma yanzu yana rayuwa da mata 17 da tulin ya'ya har 108 ciki har da Gwamna Nwifuru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ebonyi - Mahaifin Gwamna Francis Nwifuru ya zama basarake a jihar Ebonyi da ke Kudancin Najeriya.

Al'ummar yankin Oferekpe Agbaja sun nada Eze Ezekiel Nwifuru Nwankpu a matsayin Sarkinsu.

An nada mahaifin gwamna a Najeriya muƙamin sarki
Mahaifin Gwamna Francis Nwifuru ya zama sarki a jihar Ebonyi. Hoto: Rt. Hon. Francis Nwifuru Ogbonna.
Asali: Facebook

An nada mahaifin gwamna sarautar gargajiya

Daily Trust ta ruwaito cewa yan Oferekpe Agbaja sun tabbatar da nadin ne a ranar Asabar 7 ga watan Disambar 2024.

Kara karanta wannan

Ribas: Gwamna ya tuna abin da ƴan sanda suka yi, ya faɗi sarakuna 2 da aka 'wulaƙanta'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Eze Nwankpu manomi ne wanda ke da mata 17 bayan rabuwa da guda biyu wanda a halin yanzu yana da 'ya'ya 108.

Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ɗaya ne daga cikin 'ya'yan wannan sabon basarake da aka naɗa.

Eze Nwankpu zai shugabanci yankin Oferekpe Agbaja wacce ta ƙunshi ƙauyuka 17 yayin da aka yi masa ado da sandar mulki a matsayin basarake.

Wannan bikin ya gudana ne a makarantar firamare ta Oferekpe Agbaja da ke karamar hukumar Izzi a jihar Ebonyi.

Musabbabin nada mahaifin gwamna muƙamin sarauta

A jawabinsa, shugaban taron kuma tsohon Minista, Chief Godwin Ogbaga ya yaba da nadin Nwifuru Nwankpu a matsayin sarkin gargajiya na yankin.

Ogbaba ya ce an nada basaraken ne bisa gudunmawarsa wajen cigaban al'umma musamman a cikin kabilar Izhi.

Ogbaga ya ce nadin Eze Nwifuru ya samu nasara ne saboda ɗansa wanda a halin yanzu shi ne gwamnan jihar Ebonyi.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Najeriya sun yi Allah wadai da tashin bam a jihar Zamfara

Gwamna Nwifuru ya kori kwamishinansa

Kun ji cewa Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya ci gaba da nuna halin rashin son wasa da aiki daga wajen kwamishinoninsa.

Francis Nwifuru ya sake ɗaukar matakin ladabtarwa, ya dakatar da wani daga cikin kwamishinonin da ke aiki a ƙarƙashinsa.

Ya zuwa yanzu dai gwamnan ya dakatar da kwamishinoni guda huɗu bayan ya zarge su da aikata laifuffuka daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.