Yajin Aiki: Gwamna Ya Fusata, Ya Yi Barazanar Korar Ma'aikata cikin Kwanaki 3
- Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru ya yi barazanar maye gurbin duk ma'aikatan da suka biyewa NLC suka shiga yajin aiki a jihar
- A wani jawabin kai tsaye da ya yi, gwamnan ya fusata da matakin NLC duk da ya fara biyan sabon mafi karancin albashin N75,000
- Francis Nwifuru ya ce duk ma'aikacin da ya biyewa NLC, zai dakatar da albashinsa kuma ya maye gurbinsa a kwanaki uku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya sha alwashin dakatar da albashi da maye gurbin duk ma'aikacin da shiga yajin aiki tare da kungiyar NLC.
Gwamnan ya yi wannan barazana ne a wani jawabin kai tsaye da ya yi ga al'ummar jihar Ebonyi ranar Litinin, 2 ga watan Disamba, 2023 a Abakaliki.
Tribune Nigeria ta tattaro cewa a karshen makon nan, ƙungiyar kwadago (NLC) ta umarci ma'aikata a Ebonyi su fara yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Nwifuru ya fusata da yajin-aikin NLC
Sai dai Gwamna Nwifuru ya fusata da yunkurin NLC ta reshen jihar Ebonyi na shiga yajin aiki duk da ya fara biyan sabon albashi.
Gwamnan dai ya fara biyan sabon albashi na N75,000 ga ma'aikatan da ke mataki na daya da na biyu da kuma ƙarin N40,000 ga ma'aikatan da suka kai mataki na uku zuwa 17.
A jawabin da ya yi, gwamnan Ebonyi ya ce ba wai zai dakatar da albashinsu kaɗai ba ne, zai maye gurbin duk ma'aikacin da bai fita ofis ba na tsawon sa'o'i 72.
Gwamnan Ebonyi ya yi barazanar maye gurbin ma'aikata
A cewarsa, ya gatanta ma'aikatan gwamnati a Ebonyi don haka babu dalilin da ƴan kwadago za su tafi yajin aiki, Daily Trust ta rahoto.
"Idan ku ka daina zuwa ofis, ba wai zan daina biyanku albashi ba ne, zan maye gurbinku cikin sa'o'i 72," in ji shi.
Gwamnan Ebonyi ya kori kwamishinoni 2
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi ya dakatar da wasu kwamishinoni biyu daga aiki kan zargin rashin ɗa'a da sakacin aiki.
Kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Jude Chikadibia-Okpor ya bayyana hakan a sanarwar da aka rabawa manema labarai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng