Ana Jimamin Rasa Rayuka a Zamfara, Ana Zargin 'Bam' Ya Tarwatse da Wani a Niger
- An shiga fargaba yayin da wani manomi ya rasa ransa bayan abin fashewa ya tarwatsa shi a jihar Niger da ke Arewacin Najeriya
- Rahotanni sun tabbatar da lamarin ya faru ne a yau Asabar 7 ga watan Disambar 2024 yayin da marigayin ke dawowa daga gona
- Wannan na zuwa ne kwanaki ƙadan bayan rasa rayukan wasu mutane a Zamfara sanadin fashewar 'bam' a yankin Dansadau da ke jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Niger - An shiga alhini bayan wani manomi ya rasa ransa a wani fashewar 'bam' a Bassa da ke karamar hukumar Shiroro da ke jihar Neja.
Lamarin ya faru ne a yau Asabar 7 ga watan Disambar 2024 inda ya rutsa da manomin mai suna Isyaku Gambo.
Niger: Ana zargin 'bam' ya hallaka manomi
Daily Trust ta ruwaito cewa marigayin ya taka wani abu mai fashewa da ake zargin an dasa a kan hanyar kauyen Unguwan-Usman da Bassa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tabbatar da cewa manomin yana tafiya a kan babur ne dauke da kayan gonarsa zuwa garin Bassa.
Wani ganau ya bayyana cewa fashewar ta tarwatsa jikin mamacin gaba daya nan take ba tare ba ta lokaci ba.
Yadda 'bam' ya hallaka manomi a Nigeria
“Abin ya faru ne yau Asabar misalin karfe 3 na rana, lokacin da marigayin ke dawowa daga gona."
"Ya tafi dauko kayan amfanin gona zuwa gida, wannan shi ne karo na farko da muke fuskantar irin wannan."
"Ana zargin cewa 'yan ta’adda ne suka dasa abun fashewar."
- Cewar majiyar
Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun bai mayar da martani ga sakon yan jaridu ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Ana zargin 'bam' ya hallaka mutane a Zamfara
A baya, kun ji cewa wata motar haya dauke da fasinjoji ta taka wani abu da ake zargin 'bam' ne wanda ya jawo ta tarwatse tare da ajalin mutane 12.
Wannan ne karo na biyu a mako guda da abin fashewa ta tashi a kan hanya, wanda ke barazana ga matafiya a yankin Dansadau.
An nemi gwamnati da ta dauki matakin gaggawa yayin da aka yi kira ga jama'a da su yi taka tsantsan a lokacin tafiye-tafiyensu.
Asali: Legit.ng