Arewa da Kudu: Yadda Kudurin Harajin Tinubu Ya Raba kan ’Yan Majalisa da Manyan Najeriya

Arewa da Kudu: Yadda Kudurin Harajin Tinubu Ya Raba kan ’Yan Majalisa da Manyan Najeriya

  • Ana ci gaba da cece-kuce kan kudurin haraji da aka gabatar a gaban majalisar Najeriya don duba tare da tabbatarwa nan kusa
  • ‘Yan Arewa da dama sun nuna adawa da kudurin, lamarin da ya kawo sabani da rabuwar kai a majalisar dattawa ta Najeriya
  • Rahoto ya bayyana kadan daga abin da kudurin ya kunsa da kuma abin da wasu manyan Najeriya keg ani game da kudurin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Najeriya - Kudurin sauya haraji da ke gaban Majalisar Dattawan Najeriya ya janyo cece-kuce mai tsanani a tsakanin ’yan majalisar daga Arewa.

Rahotanni sun bayyana cewa, wasu daga cikin ’yan majalisar sun goyi bayan kudurin, yayin da wasu suka nuna adawa da shi tare da bayyana sukarsa a fili.

A ranar 3 ga Oktoba, Shugaban Kasa Bola Tinubu ya gabatar da kudurorin sauya haraji hudu ga Majalisar Dokoki ta Kasa.

Yadda sabani ya dabaibaye majalisar kasa
Majalisar kasa ta shiga sabani kan kudurin haraji | Hoto: @SenateNGR
Asali: Facebook

Wannan ya hada da Kudirin Kafa Hukumar Hadin Kai Kan Haraji, Kudirin Kafa Hukumar Haraji ta Najeriya, da Kudirin Haraji na Najeriya na 2024.

Kara karanta wannan

Shugabannin Arewa sun nemo mafita kan kudirin haraji, ana tattaunawa domin kare yankin

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnoni sun nuna adawa da kudurin

Gwamnonin Arewa sun nuna adawarsu da kudurin, suna masu cewa zai cutar da tattalin arzikin yankin. Sun ce tsarin da ake shirin aiwatarwa zai fi bai wa jihohin kudu alfanu fiye da na Arewa.

A wani zama na majalisar, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Jibrin Barau, ya umarci a dakatar da duk wani aiki kan kudurorin harajin da aka gabatar.

Sai dai, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya soke wannan umarnin, yana mai cewa kudurin ba a janye shi ba tukuna.

A bangarensa, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya yi kakkausan suka ga kudurin. Ya bayyana cewa idan aka aiwatar da shi, zai durkusar da tattalin arzikin Arewa da ke dogaro da noma.

‘Yan majalisar Arewa na adawa da kudurin haraji

Wasu ’yan majalisar daga Arewa sun bayyana cewa ba dukkan su ke adawa da kudurin ba. Sun ce adawar da ake gani daga wasu ’yan majalisar ta fito ne daga rashin daidaito a tsarin raba kudaden VAT.

Kara karanta wannan

'Ku kwantar da hankalinku': Sultan kan kudirin haraji bayan ganawa da Ribadu

Sanata Shehu Buba daga Bauchi ya tabbatar da cewa sun gana da gwamnonin Arewa domin samun matsaya kan kudurin.

A rahoton da jaridar ta wallafa, ta naqalto yadda yace sun bukaci Shugaban Kasa ya dakatar da kudurin domin a kara yin nazari a kai sosai.

Haka nan, Sanata Ali Ndume daga jihar Borno ya a cimma matsaya cewa za a shawarci Shugaban Kasa kan gyaran kudurin, tare da yi mata duba mai zurfi.

Yadda manyan Arewa ke ganin lamarin

Kungiyar League of Northern Democrats, karkashin tsohon Gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau, ta kafa kwamitin nazari kan kudurin.

Kungiyar ta ce za ta gabatar da rahoto cikin mako guda kan abin da ya dace a gyara a tattare da wannan kuduri mai cike da sarkakiya.

A cewar wata majiya, akwai yiwuwar kudurin zai wuce matakin sauraron jama’a tare da wasu gyare-gyare da za su tabbatar da adalci ga kowa.

Kara karanta wannan

Sanatoci 16 daga shiyya 1 sun hada kai, sun goyi bayan Tinubu kan gyaran haraji

Halin da ake ciki game da kudurin haraji

Wasu dattawa sun bayyana cewa idan aka yi watsi da kudurin ba tare da shawarwari masu kyau ba, Arewa za ta rasa tasiri a tsarin.

Duk da cece-kucen da ke tattare da kudurin, wasu daga cikin dattawan Arewa sun ce za su tabbatar da cewa kudurin ya tsaya daram tare da gyare-gyaren da za su amfani kowa.

Sai dai, fadar Shugaban Kasa na bayyana alfanu tare da wanke kai daga duk wani suka da ake yi kan wannan kuduri na gwamnatin Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.