Hafsan Hafsoshi Ya Gano Bakin Zaren kan Samar da Tsaro a Najeriya

Hafsan Hafsoshi Ya Gano Bakin Zaren kan Samar da Tsaro a Najeriya

  • Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya (CDS), Janar Christopher Musa, ya taɓo batun samun tsaron ƙasa a Najeriya
  • Janar Christopher Musa ya yi nuni da cewa ƙarfin sojoji kaɗai ya yi kaɗan wajen samar da tsaron ƙasa a Najeriya
  • Hafsan hafsoshin ya bayyana cewa bayan ayyukan sojoji, akwai sauran abubuwan da ake buƙata domin cimma hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya (CDS), Janar Christopher Musa, ya yi magana kan tsaron Najeriya.

Janar Christopher Musa ya jaddada cewa ayyukan sojoji kaɗai ba za su iya cimma tsaron ƙasa a Najeriya ba.

CDS ya yi magana kan tsaron Najeriya
Janar Christopher Musa ya tabo batun tsaron Najeriya Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Janar Musa ya bayyana haka ne yayin taron tattaunawa kan harkokin tsaro, wanda aka shirya a birnin Abuja, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cibiyar yaƙi da ta’addanci ta ƙasa karkashin ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, tare da hadin gwiwar ƴan jaridun hedkwatar tsaro suka shirya taron a Abuja.

Kara karanta wannan

'Babban dalilin da ya sa ƴan Majalisar Tarayya 4 suka sauya sheka zuwa APC'

Me hafsan hafsoshi ya ce kan tsaron Najeriya?

A cewarsa, aikin sojoji kaso 30% ne kawai na abin da ake buƙata domin samun tsaron ƙasa, yayin da sauran kaso 70% ya dogara ne kan harkokin siyasa da zamantakewa.

"A cikin duniyar da ke cike da tashe-tashen hankula, rashin tabbas, matsalolin tsaro, rikice-rikice, ana taƙaita batun tsaron ƙasa daga wata ƙaramar mahanga."
"Abu ne mai sauƙi a iya gano cewa, an maida da hankali kan harkokin tsaron ƙasa ne a kan tattaunawa kan ƙarfin sojoji da kuma barazanar da masu tayar da ƙayar baya ke yi."
"Har ila yau, ya kamata a lura da cewa ayyukan da sojoji suke yi wajen tabbatar da tsaron Najeriya, kaso 30% ne kacal na duk ƙoƙarin da ake bukata."
"Yayin da sauran kaso 70% cikin 100% na wanzar da zaman lafiya da tsaron Najeriya ya rataya ne a kan al’amuran zamantakewa."

Janar Christopher Musa

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba Faransa damar kafa sansanin sojoji a Arewa? Rundunar tsaro ta magantu

Hafsan tsaro ya magantu kan kafa sansanin soja

A wani labarin kum, kun ji cewa babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya yi magana kan jita-jitar kawo sojojin Faransa zuwa ƙasar.

Janar Christopher Musa ya ƙaryata rahotannin da ke cewa an ba Faransa izinin kafa sansanin sojojin ƙasashen waje a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng