Daga Dawowa Najeriya, Tinubu Ya Shiga Yin Nade Naden Mukami a Hukumar Raya Arewa

Daga Dawowa Najeriya, Tinubu Ya Shiga Yin Nade Naden Mukami a Hukumar Raya Arewa

  • Bola Ahmed Tinubu ya yi nadin mukamai a hukumomin NWDC da SEDC masu alhakin raya shiyyoyin Arewa da Kudu
  • An yi wannan sauye-sauye ne domin tafiya da kowane bangare, Sanatoci za su tantance wadanda za a ba mukaman
  • Wannan nadin mukamai da aka yi zai rufe bakin masu cewa an manta su wajen ba da kujerun gwamnatin tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya canza nadin mukaman da ya yi a hukumar NWDC da aka kirkiro domin raya Arewa maso yamma.

Shugaban kasar ya aikawa majalisar dattawa wasu jeringiyar sunayen mutanen da yake so su jagoranci NWDC da takwararta watau SEDC.

Bola Tinubu
Bola Tinubu ya yi nadin mukamai a NWDC da SWDC Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Sanarwar da aka samu a shafin Olusegun Dada a dandalin X ya bayyana cewa Farfesa Abdullahi Shehu Ma’aji bai rasa kujerarsa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wannan jerin sunayen da aka aika, akwai mutane irinsu Alhaji Lawal Samai’la Abdullahi wanda ya canji Ambasada Haruna Ginsau.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi rabon mukamai, ya ba malamin musulunci matsayi a gwamnatin tarayya

Tinubu ya canza wasu mutane a NWCD

Rahoton da The Nation ta fitar dazu ya ce an maye guraben Sanata Sani Yahaya Kaura da Hon. Abdulkadir S. Usman a sabuwar hukumar.

Wadanda za su canje su kuwa su ne: Ja’afar Abubakar Sadeeq da Yahaya Aminu Abdulhadi.

NWCD ta samu wakilci daga kowane yanki

Kamar yadda dokar kasa ta tanada, shugabannin hukumar raya yankin Arewa maso yamman ya kunshi mutane daga kowane yanki.

Wannan karo shugaban kasa Bola Tinubu ya ba da sunayen Chukwu Chijioke, Ahmed Mohammed da Injiniya Ahmed Rufai Timasaniyu.

Sannan za a tantance Macdonalds Michael Uyi, Yemi Ola da kuma Honarabul Babatunde Dada.

Hukumar SEDC ta samu shugabanni

Sai a SEDC da aka kirkiro domin cigaban Kudu maso gabas, Hon. Emeka Atuma da Hon. Mark C. Okoye ne za su jagoranci aikin hukumar.

A majalisar hukumar akwai Barista Ugochukwu H. Agballah, Hon. Okey Ezenwa, Cif Hyacinth Ikpor da Hon. Donatus Eyinnah Nwankpa.

Kara karanta wannan

Za a yi aikin sama da Naira Tiriliyan 4 a masarautar Arewa da ta nada Tinubu Jagaba

Sai Barr. Ifeanyi Agwu, Nasiru Usman, Hamma Adama Ali Kumo, Edward David Onoja, Orure Kufre Inima da Joke Adebayo-Chukwuma.

Cikin wadanda majalisar dattawa za ta tantance akwai Prince Obinna Obiekweihe, Anthony O. Agbo da Dr. Daniel Ikechukwu Ugwuja.

Bola Tinubu ya yi nadin mukamai

Mai taimakawa shugaban kasa wajen yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar da sanarwa an nada shugabannin hukumomi.

Bola Ahmed Tinubu ya nada Farfesa Abdullahi Yusuf Ribadu ya zama sabon shugaban NUC, kuma Farfesa Salisu Shehu ya samu mukami.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng