Sheikh Muyideen: Muhimman Abubuwa 4 game da Malamin Musulunci da Ya Rasu

Sheikh Muyideen: Muhimman Abubuwa 4 game da Malamin Musulunci da Ya Rasu

  • Sheikh Muyideen Ajani Bello wanda aka haifa a Ibadan, jihar Oyo ya sadaukar da rayuwarsa wajen yada addinin Musulunci
  • A lokacin da ya cika shekara ta 10, Sheikh Bello ya fara wa’azi, wanda ya kai ga an yi masa nadin sarautar "Sulthonil Waa’izeen"
  • Sheikh Bello ya rasu yana da shekaru 84, amma koyarwarsa za ta ci gaba da zama abin koyi a tsakanin Musulmai a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - Sheikh Muyideen Ajani Bello, wanda aka fi sani da "Baba Oniwasi Agbaye," fitaccen malamin addinin Musulunci ne a Najeriya, an haife shi a Ibadan, Jihar Oyo.

Sheikh Muyideen Ajani Bello ya sadaukar da rayuwarsa wajen yada addinin Musulunci, inda ya zama abin girmamawa a cikin al’ummar Musulmai.

Sheikh Muyideen ajani Bello: Allah ya yiwa fitaccen malamin Musulunci rasuwa.
Abubuwa 4 game da marigayi Sheikh Muyideen ajani Bello. Hoto: @Advsola
Asali: Twitter

Legit Hausa ta tattaro wasu muhimman abubuwa hudu da ya kamata ku sani game da marigayi Sheikh Muyideen Ajani Bello.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya kaɗu da rasuwar babban malamin addinin Musulunci a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Sheikh Muyideen ya fara wa'azi a 1950

An haifi Sheikh Muyideen a Ibadan a shekarar 1940, kamar yadda rahoton Daily Trust ya nuna.

Mahaifinsa malamin addini ne wanda ya sanya masa sha’awar karatun addini tun yana dan karami.

A lokacin da ya cika shekaru 10, Sheikh Bello ya fara wa’azi ga jama’a, wanda hakan ya kasance farkon sadaukarwarsa ga yada addinin Musulunci.

2. An yi wa Sheikh Muyideen nadin sarauta

Sheikh Bello ya samu girmamawa saboda tsayuwa kan koyarwar Musulunci da kyawawan dabi’u.

Ya yi wa’azi a wurare daban-daban, inda yake yawan jan hankalin jama’a kan bin koyarwar Musulunci.

A watan Afrilu 2024, majalisar koli ta malaman Musulunci a Kudu maso Yammacin Najeriya ta naɗa shi sarautar "Sulthonil Waa’izeen" (Sarkin masu wa'azi) na kasar Yarabawa.

3. Kalubalen da Sheikh Muyideen ya fuskanta

A tsawon hidimarsa ga addinin Musulunci, Sheikh Bello ya gamu da kalubale daban daban, amma ya jajurce tare da ci gaba da wa'azi.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun yi martani da duniyar Musulunci ta yi babban rashin malamin addini

A lokacin da yake jihar Oyo kuwa, Sheikh Muyideen ya ce ya tsorata da labarin fatalwa da ake ake yi a kasuwa, da kuma yawan ganin gawarwaki a Abeokuta, wanda ya sa shi komawa Kano.

A wata hira da aka yi da shi, wadda shafin Oyo Insight ya wallafa, malamin ya ce babban kalubalen da ya fuskanta a komawarsa Kano shi ne rashin iya Hausa.

Malamin ya ce an amince masa ya koyar da yara karatu a Kano, amma su yaran ba sa jin Turanci, shi kuma ko kusa ba ya jin yaren Hausa.

4. Rasuwar Sheikh Muyideen Ajani Bello

Sheikh Muyideen ya rasu a ranar 6 ga Disamba, 2024, yana da shekaru 84 kenan a duniya.

Dansa, Katibi Abdul Basit Olanrewaju (Aponle Anobi) da Sheikh Taofeeq Akewugbagold, suka tabbatar da rasuwarsa.

An tabbatar da cewa koyarwarsa za ta ci gaba da ba da gudunmawa ga Musulmai a Najeriya.

Kara karanta wannan

'Ana shirin markaɗe mu': Malamin addini ya hango 'makircin' da ake kullawa Arewa

Gwani Muhammad Sani ya rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Allah ya karbi rayuwar gogaggen mahaddaci kuma mai masanin Al-Qur'ani a Arewa, Gwani Muhammad Sani.

Gwani Muhammad Sani wanda ya rasu a jihar Gombe an ce ya shafe shekaru yana karantar da ɗalibai Alkur'ani daga dukkan sassan Arewacin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.