Ya kamata a koyar da yara da asalin yarensu, ba yaren aro ba, inji wani marubuci

Ya kamata a koyar da yara da asalin yarensu, ba yaren aro ba, inji wani marubuci

- Wani marubuci ya yi tsokaci cikin littafinsa kan yadda za a kiyaye al'adu a kasashen Afrika

- Marubucin ya bayyana ra'ayinsa na karantar da yara kanana da asalin yarensu ya fi dacewa

- Hakazalika ya bada hujjarsa da cewa, a shekaru hudu zuwa goma ne yara suke koyan komai

Wani marubuci, Mista Tony Olaniji, ya ba da fatawar a koyar da yara a cikin harshen gida, yana mai cewa hakan zai inganta karatu da rubutu, The Punch ta ruwaito.

Olabanji, a gaban gabatarwar littafinsa, ‘Kíyèsi - A Collection of African Stories for Children,’ ya ce koyar da yara cikin yarensu na asali zai taimaka wajen kiyaye al’adun mutane.

Ya ce, “Idan kuka bincika sosai, yawancin abin da muke zama yanzu mun same shi ne a shekarun da muka fara koyo, musamman daga shekaru huɗu zuwa 10.

KU KARANTA: Su Burutai su godewa Allah ba lokacin da muke majalisa bane, in ji Shehu Sani

Ya kamata a koyar da yara da asalin yarensu, ba yaren aro ba, inji wani marubuci
Ya kamata a koyar da yara da asalin yarensu, ba yaren aro ba, inji wani marubuci Hoto: The Albert Baker Fund
Asali: UGC

"Duk wani adabi, nishaɗi da ilimi da yaro ya nuna a wannan matakin yana da mahimmanci. Na ji ina karanta littattafai kuma lokaci ya yi da zan ba da gudummawata ga tushen ilimin.

“Yara sune manyan gobe, a lokacin da suka girma, babu abinda za ku iya sake yi. Matakin yara shi ne lokacin da za ku koya masu kyawawan dabi'u.”

Marubucin ya ce an zabi taken littafin ne domin jaddada mahimmancin bada hankali.

“Kalmar Kiyesi tana nufin cewa ka mai da hankali sosai ga wani abu. Me muke mai da hankali akai? Muna mai da hankali kan yara saboda suna da rauni.

"Don tabbatar da cewa al'adunmu ba su lalace ba, ya kamata mu koma ga asali. An koyar da mu sosai da yarenmu na asali a makarantar firamare,” in ji Olaniji.

Mai nazarin littafin, Mista Folu Agoi, ya ce littafin ya kunshi tatsuniyoyi guda bakwai masu kayatarwa wadanda aka zakulo su daga muhallin Yarbanci na yankin.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Majalisa ta shiga zaman tantance sabon shugaban EFCC, Rasheed Bawa a yau

A wani labarin, Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Misis Amina Mohammed ta roki Gwamnatin Tarayya ta kara sanya jari a kan matasa a matsayin wata hanya ta magance rashin tsaro, a rahoton Channels Tv.

Da take magana yayin ziyarar girmamawa ga Ministan Harkokin Wajen Najeriya Mista Geoffrey Onyeama, Misis Amina ta lura cewa ya kamata a bai wa matasa da sauran ‘yan Nijeriya wani abin da za su sa ido domin bayar da gudummawa ga ci gaban kasar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel