Malamin Musulunci Ya Fadi Abin da Ake Tunkara a Najeriya da Ya Fi Kudirin Haraji Masifa

Malamin Musulunci Ya Fadi Abin da Ake Tunkara a Najeriya da Ya Fi Kudirin Haraji Masifa

  • Yayin da ake ta magana kan sabon kudirin haraji, malamin Musulunci ya ce akwai masifar da ake tunkara da ta fi wannan a cewarsa
  • Sheikh Murtala Bello Asada ya ce alakar Bola Tinubu da kasar Faransa ba karamar fitina za ta jawo ba, musamman a jihar Sokoto
  • Malamin ya nuna damuwa kan yadda ake shirin kawo sojojin Faransa saboda hadin guiwa, ana tsoron dakarun za su shigo har Sokoto

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Sheikh Murtala Bello Asada ya yi magana kan alakar Shugaba Bola Tinubu da kasar Faransa.

Shehin malamin ya ce ana ta magana kan kudirin haraji a Najeriya akwai bala'in da ya fi wannan.

Malamin Musulunci ya koka kan masifar da ta tunkaro Najeriya bayan kudirin haraji
Sheikh Murtala Bello Asada ya nuna damuwa kan alakar Bola Tinubu da Faransa. Hoto: Malam Murtala Bello Asada, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Sheikh Bello Asada ya ce masifa na tafe

Kara karanta wannan

Kudirin Haraji: Gwamnatin Tinubu za ta rika karbar haraji a kudin gado?

Sheikh Bello Asada ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Karatuttukan Malaman Sunnah ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya ce ana kawar da hankulan mutane kan kudirin haraji amma ga masifar da ta kunno kai yanzu.

Ya ce alakar Bola Tinubu da Faransa kan hakar ma'adinai da kawo sojoji ba karamar fitina ba ce musamman a jihar Sokoto.

"Ya ku al'ummar Musulmi, wato hadarin da muke fuskanta an juyar da hankalin mutane kan maganar haraji."
"Akwai bala'in da ya fi na haraji, Bola Tinubu ya zo ya hada kai da Faransa domin kawo sojoji Najeriya a tono ma'adinai da hadin guiwa."
"Amma ku bari ku ji Sokoto na daga jihohin da za a ba sojojin Faransa mafaka saboda idan za a farwa Nijar an samu mataki."

- Sheikh Murtala Bello Asada

Malam Bello Asada ya goyi bayan Nijar

Shehin malamin ya ce duk wanda zai yaki Nijar to da su zai yi fada domin za su mara mata baya dari bisa dari.

Kara karanta wannan

'A fassara kudirin zuwa harshen Hausa': 'Dan Majalisa a Arewa ya ba da shawara

Malamin ya ce babu abin da Najeriya ta yi musu illa zalunci inda ya yi addu'ar kafin bawan Allah nan ya kashe su Ubangiji ya ga bayansa.

Sheikh Bello Asada ya kalubalanci Bello Turji

A baya, kun ji cewa Sheikh Murtala Bello Asada ya sake kalubalantar Bello Turji a wani bidiyo inda ya tabbatar da zargin ana daukar nauyin ta'addanci.

Malamin ya ce Turji a faifan bidiyo, ya tabbatar da hannun karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ɗaukar nauyin ta'addanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.