Ta Faru Ta Kare, Gwamnatin Tinubu Ta Kori Ma'aikata Masu 'Digiri 'Dan Kwatano'
- Gwamnatin tarayya ta sallami ma’aikatan da suka yi karatu a wasu jami’o’in jamhuriyyar Benin da Togo daga 2017 zuwa yau
- Kwamitin da gwamnati ta kafa ya bayar da shawarar wannan mataki domin tsaftace ma’aikatu daga masu takardun bogi
- Hukumar NYSC ta fara aiwatar da wannan umarni, an kori wasu ma'aikata da aka dauka aiki da kwalin 'digiri dan kwatano'
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin tarayya ta kori ma’aikatan da suka yi karatu a wasu jami’o’in kudi na Jamhuriyar Benin da Togo
Wannan korar ta shafi ma’aikatan da suka kammala karatun digiri daga jami’o’in kasashen biyu daga shekarar shekarar 2017 zuwa yanzu.
Daraktan sadarwa na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Segun Imohiosen, ya tabbatar da wannan mataki ga jaridar The Punch a ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnati ta kori masu digirin Benin & Togo
Rahoton jaridar ya nuna cewa ba a bayyana adadin ma’aikatan da aka kora ba, amma ana sa ran ma’aikatu da hukumomi ne za su aiwatar da hakan.
Wata majiya ta tabbatar da cewa kwamitin binciken takardun digiri da gwamnati ta kafa ya bayar da shawarar a kori ma’aikatan da abin ya shafa.
Ta ce kwamitin ya gano cewa wasu daga cikin jami’o’in suna ba da kwalin digiri alhalin matakin karatunsu bai cika ka’ida ba, wanda ya sa dole a kori ma'aikatan.
Rahoton ya ce wata wasiƙar daga ofishin sakataren gwamnatin ta umarci ma’aikatu da hukumomi su gano ma’aikatan da aka dauka aiki da digiri dan kwatano daga 2017.
An sallami ma'aikata a hukumar NYSC
Kwamitin binciken ya bayyana cewa wannan mataki yana cikin yunkurin tsaftace ma’aikatu daga matsalolin da suka shafi daukar aiki da takardun bogi.
Wasu hukumomi kamar NYSC sun fara aiwatar da wannan umarni kamar yadda aka ba su umarni daga ofishin sakataren gwamnatin.
Daraktar NYSC, Caroline Embu, ta tabbatar da cewa ma’aikata biyar ne aka sallama bayan gano suna amfani da digirin jami'o'in Togo da Benin bisa bin umarnin SGF.
Gwamnati ta waiwayi masu digiri dan kwatano
Tun da fari, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ce kwamitin bincikenta ya bankado daliban da suka mallaki digirin bogi daga jami'o'in Benin da Togo.
Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya ce akwai bukatar gano masu amfani da takardun bogi a cikin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu domin a kore su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng