Yadda Goyon Bayan Kudurin Harajin Tinubu Ya Jawo wa Sanata Barau Jibrin Suka a Arewa
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I Jibrin ya shiga matsin lambar siyasa a kwanakin nan
- Nuna goyon baya ga kudirin harajin Bola Ahmed Tinubu ya jawo masa kakkausan suka a Arewacin Najeriya
- Ana zargin Sanatan da rashin kishin yankinsa da gyara siyasarsa ta hanyar neman fada a wajen shugaban kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I Jibrin ya fusata mazauna Arewa saboda fitowa karara wajen goyon bayan kudirin harajin Tinubu.
Zargin goyon bayan duk wani abu da zai cutar da Arewa, ya na daya daga cikin abubuwan da zai iya kawo nakasu ga tafiyar dan siyasa da ya fito daga yankin.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda aka samu masu sukar Sanata Barau I Jibrin, musamman a shafukan sada zumunta bisa zargin fatali da cigaban Arewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Barau Jibrin ya gwabza da Sanata a majalisa
Guda daga dalilan da aka rika zargin Sanata Barau da rashin kishin Arewa, shi ne yadda ya rika musayar yawu da Sanata Ali Ndume da ke adawa da kudirin.
Barau, ya nuna goyon bayansa ga kudirin harajin Tinubu, inda wasu ke zargin ya yi haka ne saboda kare siyasarsa.
Sanata Barau ya sha suka a masallatai
Ana zargin siyasar Sanata Barau ta shiga wani hali, bayan an rika wa'azi a masallatan Juma'a, ana zarginsa da goyon bayan kudirin da zai kara talauta Arewa.
Fitattun masu amfani da shafukan sada zumunta, irinsu Dan Bello sun kara fito da matsayar Sanata Barau I Jibrin a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na tiktok dubban mutane su ka kalla.
Barau ya kare kan shi game da kudirin haraji
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Barau I Jibrin ya musanta zargin cewa ba shi da kishin Arewa ko son cigabanta, tare da kare kansa.
Sanata Barau I Jibrin ya kara da cewa babu yadda za a yi, ya goyi bayan wani kudiri da zai cutar da shiyyar Arewacin kasar nan da ya fito.
Sanata Barau ya goyi bayan kudirin haraji?
A baya, kun ji yadda mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I Jibrin ya nuna goyon bayansa ga kudirin harajin shugaba Bola Ahmed Tinubu da Arewa ke adawa da shi.
Duk da rashin amincewa wasu Sanatoci, kamar Ali Ndume da Abdul Ningi, Sanata Barau ya ba shugabannin kwamitin gwamnatin tarayya a kan haraji damar magana a gaban majalisa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng