Ana Ta Rigimar Haraji, Dan Majalisa daga Arewa Ya Yabawa Kokarin Tinubu, Ya Soki Buhari
- Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar mazabar Yagba a jihar Kogi, Hon. Abejide Leke ya yi magana kan salon mulkin Bola Tinubu
- Hon. Leke ya yabawa shugaban kan irin tsare-tsaren da ya kawo inda ya ce shi ne kaɗai wanda zai ceto kasar a halin da take ciki
- Dan Majalisar ya kuma caccaki gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari kan yin rugu-rugu da tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Dan Majalisar Tarayya daga jihar Kogi ya yabawa tsare-tsaren Bola Tinubu wurin inganta Najeriya.
Hon. Abejide Leke da ke wakiltar mazabar Yagba ya ce babu wanda zai ceto Najeriya sai Shugaba Tinubu.
'Dan Majalisar Tarayya ya soki tsarin Buhari
'Dan Majalisar ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a yau Laraba 4 ga watan Disambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hon. Leke ya kuma caccaki gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari kan zargin lalata tattalin arziki da mayar da kasa baya.
Matashin dan Majalisar ya ce komai ya lalace musamman a babban bankin Najeriya, CBN karkashin jagorancin Godwin Emefiele a wancan lokaci.
Abejide ya kora yabo ga tsare-tsaren Tinubu
"Zuwa shekarar 2026 idan aka dubi kasa, kowa zai rika yabawa Bola Tinubu saboda shi kadai ne zai iya ceto Najeriya a halin da take ciki."
"A karshen mulkin gwamnatin da ta shude, samun N1,000 zai maka wahala, ka san takardun Naira nawa aka buga a CBN? Ta yaya tattalin arziki zai bunkasa a haka?"
- Hon. Abejide Leke
'Dan Majalisa ya bukaci fassara kudirin haraji
A baya, kun ji cewa duba da cigaba da korafi kan kudirin haraji da ake ta yi a Najeriya, dan Majalisar Tarayya ya yi korafi kan yan Arewa.
'Dan Majalisar daga jihar Kogi, Hon. Abejide Leke ya ce mafi yawan masu korafin suna yi ne saboda siyasa da zaben 2027 saboda illata Bola Tinubu.
Hon. Leke ya shawarci a fassara kudirin zuwa harshen Hausa duba da yadda matsalar ta fi yawa a Arewacin Najeriya fiye da Kudancin kasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng