Ana Ta Maganar Haraji, Kano Ta Dawo da Rusau, An Shata Wurare da Aka Gina Babu Ka'ida

Ana Ta Maganar Haraji, Kano Ta Dawo da Rusau, An Shata Wurare da Aka Gina Babu Ka'ida

  • Gwamnatin jihar Kano ta cigaba da rushe wasu gine-gine da kadarori da aka gina su a wuraren da aka ware na hukuma
  • Gwamnatin ta dauki matakin ne domin kwato wasu filaye na gwamnati da al'umma suka yi gine-gine ba bisa ka'ida ba
  • Shugaban hukumar da ke rushe-rushen, Hameed Sidi ya ce sun gano wurare da dama a 'Kwankwasiyya City' da aka yi gini babu ka'ida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta dawo da maganar rusau a kan gine-gine da aka yi ba bisa ka'ida ba.

Gwamnatin jihar ta dauki matakin ne kan wasu gine-gine da aka yi a kan filaye na gwamnati wanda hakan saba doka ne.

Gwamnatin Kano ta sake dawo da maganar rusau, an rushe wasu kadarori
Gwamnatin Abba Kabir ta rushe wasu gine-gine a 'Kwankwasiyya City' da ke Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Gwamnatin Abba Kabir ta sake yin rusau

Kara karanta wannan

Sultan da shugaban CAN sun ajiye bambancin addini, sun mika bukata 1 ga Tinubu

Sakataren Hukumar kula da cigaban jihar Kano, Hameed Sidi shi ya tabbatar da haka a 'Kwankwasiyya City', cewar Daily Nigerian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sidi ya ce hukumar ta fi mayar da hankali kan gine-gine da aka yi su ba tare samun amincewar gwamnati ba.

Shugaban hukumar ya ce sun dauki matakin ne domin kwato filayen gwamnati da aka tanadar domin gina abubuwan cigaba.

Ya ce kwamitin ya gano fiye da gine-gine guda 10 da aka yi ba bisa ka'ida ba a 'Kwankwasiyya City', The Guardian ta ruwaito.

Har ila yau, Sidi ya ce hukumar za ta mayar da hankali kan wuraren da suka yi kaurin suna wurin gine-gine ba bisa ka'ida ba.

Sidi ya tabbatar da cewa an ba masu kadarorin wa'adi kafin fara wannan rushe-rushe da ake yi a jihar.

Gwamnatin Kano ta shawarci al'umma kan filayensu

"Mun himmatu wurin tabbatar da kawo sauyi da kuma yin abin da ya dace domin yin amfani da wuraren gwamnatin kan dalilin da aka samar da su."

Kara karanta wannan

'Kudirin haraji zai iya jefa Najeriya a tashin hankali,' Dattijo ya yi gargadi

- Hameed Sidi

Sidi ya shawarci al'umma da su garzaya ma'aikatar filaye da safiyo domin sabunta takardun filayensu da suka tsufa.

Kano: Yan kasuwa sun yi korafi kan rusau

A baya, kun ji cewa wasu yan kasuwa a Kano da ke kan titin Jami'ar Bayero sun yi korafi kan kokarin ruguza musu wuraren sana'a da gwamnatin ke shirin yi.

Wani dan kasuwa, Ibrahim Mu'azzam ya bayyana halin da suke ciki da kuma yin kira ga gwamnatin Abba Kabir Yusuf kan lamarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.