Gwamna Ya Ji Kukan Ƴar NYSC da Malama Ta Lakadawa Duka a Ilorin, Ya Dauki Mataki
- Gwamnatin Kwara ta rage matsayin malama Fatimoh Nike saboda fada a wajen aiki da kuma lakadawa 'yar NYSC dukan tsiya
- Gwamnatin ta ce za ta tura malamar zuwa wata makaranta tare da ba ta horo kan kyawawan dabi’u domin gyara halayenta
- Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya yi alkawarin kare martabar NYSC tare da tabbatar da cewa ba za a sake samun irin haka ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kwara - Gwamnatin jihar Kwara ta ɗauki mataki kan malamar da aka zarga da cin zarafin wata 'yar NYSC a makarantar sakandare ta GJSS Kulende a Ilorin.
Sanarwar ta fito ne daga kwamishiniyar Ilimi, Hajiya Sa’adatu Modibbo Kawu da shugaban hukumar koyarwa, Mallam Bello Tauheed Abubakar.
Sanarwar da aka wallafa a shafin gwamnatin Kwara na dandalin X ya ce kwamitin binciken lamarin ya samu malama Hajiya Hamzat Fatimoh Nike da aikata laifin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An hukunta malama saboda dukan 'yar NYSC
Sanarwar ta ce kwamitin ya kama Malama Fatimoh da aikata laifuffukan da suka shafi yin fada a cikin makarantar yayin da take bakin aikinta.
An kuma same ta da yin maganganun batanci, rashin ladabi da rashin girmama alamar martabar kasa da rigar NYSC ke wakilta.
Bisa ga shawarwarin da kwamitin ya bayar, gwamnatin Kwara ta rage matakin aikin Malama Fatimoh da daraja biyu domin zama hukuncin laifin da ta yi.
Gwamnatin Kwara ta ba hukumar NYSC hakuri
Gwamnatin jihar Kwara ta kuma ce za a tura malamar zuwa wata makaranta daban tare da ba ta horo kan kyawawan dabi’u yayin aikinta.
Sanarwar ta ce gwamnati ta yi nadama kan abin da ya faru tare da tabbatarwa hukumar NYSC cewa hakan ba zai sake faruwa ba.
Yayin da gwamnatin ta ce abin da malamar ta yi ba ya wakiltar mutanen jihar, sanarwar ta ce Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya yi alkawarin kare martabar hukumar NYSC.
An lakadawa 'yar NYSC duka a Kwara
Tun da fari, mun ruwaito cewa hukumar kula da masu bautar kasa ta Allah wadai da wasu malaman sakadanre a jihar Kwara da suka lakadawa wata 'yar NYSC dukan tsiya.
An ce rigima ta kaure lokacin da 'yar bautar kasar ta je makarantar karbar wata takarda, malamai suka yi ikirarin cewa ba ta gaishe da su ba, wanda ya sa suka ci zarafinta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng