An Tarwatsa Maboyar Shugaban 'Yan Ta'adda, An Kama Gagararrun 'Yan Bindiga

An Tarwatsa Maboyar Shugaban 'Yan Ta'adda, An Kama Gagararrun 'Yan Bindiga

  • Jami’an ‘yan sanda a jihar Imo sun yi nasarar tarwatsa maboyar ‘yan ta’adda a ƙaramar hukumar Okigwe
  • Kwamishinan ‘yan sanda, Aboki Danjuma ya tabbatar da kama wasu gagararrun masu laifi a yayin farmakin
  • Jami’an tsaro sun yi kira ga al’umma su cigaba da bayar da bayanai domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar - Rundunar ‘yan sanda ta jihar Imo ta cimma babbar nasara wajen yaki da ta’addanci, ta tarwatsa wata maboyar 'yan ta’adda da ke Aku, a ƙaramar hukumar Okigwe.

Rahotanni na nuni da cewa maboyar da aka tarwatsa tana da alaƙa da wani shugaban ƙungiyar ESN mai suna “Gentle.”

Yan sanda
An tarwatsa maboyar 'yan ta'adda a Imo. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

The Nation ta ruwaito cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aboki Danjuma ya ce nasarar ta biyo bayan wani dogon bincike da suka gudanar ne a cikin makonni.

Kara karanta wannan

Peter Obi: Jam'iyyar LP ta fara shiri a jihohi 36 domin kawar da Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tonawa ‘yan ta’adda asiri a jihar Imo

Jami’an tsaro sun gudanar da wani samame a Aku, suka tarwatsa wata maboyar da ake zargin tana da alaƙa da shugaban ƙungiyar ESN.

Daily Post ta wallafa cewa 'yan sanda sun ce maboyar ta kasance matsugunni na taruwar 'yan ta’adda a yankin.

A cewar Kwamishinan ‘yan sanda, farmakin ya haifar da kama wasu gagararrun 'yan ta'adda da ke da hannu wajen ayyukan ta’addanci da suka addabi jama’a a yankin.

Jami'an tsaro sun yi hadin gwiwa a Imo

Kai farmakin ya samu hadin gwiwar manyan jami’an tsaro ciki har da kwamandan rundunar soji ta 34, Birgadiya Janar U.A. Lawal da kuma daraktan hukumar DSS.

Hadin kai tsakanin hukumomin tsaro ya kasance muhimmin abin da ya ke taimakawa wajen dakile ta’addanci da kuma tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a jihar Imo.

Kira ga jama’a domin hadin kai

Kara karanta wannan

Sultan da shugaban CAN sun ajiye bambancin addini, sun mika bukata 1 ga Tinubu

Kwamishinan ‘yan sanda, CP Aboki Danjuma ya yi kira ga mazauna jihar su bayar da goyon baya ta hanyar samar da bayanai masu amfani ga hukumomin tsaro.

Mataimaki na musamman ga gwamna kan harkokin tsaro, Birdadiya Janar Joseph Ogbonna (mai ritaya) ya tabbatar wa mazauna Aku cewa ana daukar matakan kare rayuka da dukiyoyinsu.

Kwara: An kama mai taimakon 'yan bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni da suka fito daga Kwara sun tabbatar da cewa wasu miyagu sun sace wata uwa da ‘ya’yanta biyu a yankin Ajase-Ipo.

Sai dai bayan kokarin jami'an hukumar NSCD, an samu nasarar kama wanda ake zargi da ba wa masu garkuwar bayanai, Abu Usman Soja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng