'Yan Bindiga Sun Kashe Babban Malamin Addini a Arewa, Sun Yi Garkuwa da Mutane 3

'Yan Bindiga Sun Kashe Babban Malamin Addini a Arewa, Sun Yi Garkuwa da Mutane 3

  • 'Yan bindiga sun kashe Apostle Ranti Ige-Daniel a Isanlu, jihar Kwara yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa wajen jana'iza
  • An ce faston ya ziyarci garin Isanlu domin yin wa’azi kuma an kai masa hari wajen tafiya zuwa jana'iza bayan kammala wa'azin
  • 'Yan bindigar sun kuma yi garkuwa da mutum uku daga cikin malamin inda suke neman kudin fansa na Naira miliyan 30

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara - 'Yan bindiga sun kashe wani babban fasto, Apostle Ranti Ige-Daniel, na cocin Royal Assembly Sanctuary bayan kammala wa'azi a jihar Kwara.

An ce 'yan bindigar sun farmaki malamin a kan hanyar garin Idofin zuwa Makutu lokacin da yake tare da wasu mutane uku a cikin motarsa.

Mazauna Kwara sun shiga jimami bayan 'yan bindiga sun kashe babban malamin addinin Kirista.
'Yan bindiga sun kashe malamin addini tare da sace mutum 3 a jihar Kwara. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

'Yan bindiga sun kashe fasto a Kwara

Kara karanta wannan

Kwana 70 babu wutar lantarki: 'Yan kasuwar Kano sun yi gangamin sallar Alƙunuti

Jaridar Daily Trust ta ce malamin cocin ya halarci wa'azi a garin Isanlu a ranar Talata, kuma an kai masa hari a kan hanyarsa ta zuwa jana'iza bayan kammala wa'azin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya ta ce 'yan bindigar sun buɗe wuta kan motar faston da misalin ƙarfe 8:30 na dare, inda suka kashe shi nan take.

Bayan kashe shi, 'yan bindigar sun sace mutum uku da ke a cikin motar, ciki har da wata mace da ake zaton budurwarsa ce.

'Yan bindigan na neman Naira miliyan 30

Majiyar kusa da iyalan faston ta ce 'yan bindigar sun ja gangar jikin malamin tare da sauran mutanen uku zuwa cikin daji.

Rabaran Francis Iselowo, makusanci ne ga iyalan, ya tabbatar da cewa faston da wasu uku suna kan hanyarsu ta zuwa jana'iza a Isanlu lokacin da 'yan bindigar suka farmake su

Iselowo ya shaida cewa 'yan bindigar sun nemi Naira miliyan 30 a matsayin kudin fansar mutane ukun da ke tsare a hannunsu.

Kara karanta wannan

Sultan da shugaban CAN sun ajiye bambancin addini, sun mika bukata 1 ga Tinubu

Miyagun 'yan bindiga sun sace malamin addini

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da Fasto kuma shugaban cocin RCCG, Olugbenga Olawore a kan hanyarsa ta zuwa Legas.

An ce lamarin ya faru ne a lokacin da 'yan bindigar suka tare wata motar bas da malamin ke a cikinta, a hanyarsa ta zuwa birne mahaifiyarsa ta da rasu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.