Harajin EMTL: Masu Sana'ar POS Sun Sanar da Sabon Farashin Cirewa da Tura Kudi
- Masu POS sun sanar da 'yan Najeriya cewa sun kara kudin da suke karba saboda cire harajin EMTL da bankunan intanet suke yi
- Daga ranar 2 ga watan Disambar 2024, masu sana'ar POS sun canja farashin da suke karba na hada hadar kudin da suka kai N10,000
- Wannan dai na zuwa ne yayin da FIRS ta fara cire N50 kan duk wani kudi da aka turawa bankunan intanet da ya haura N10,000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Masu sana'ar POS sun ƙara kuɗin da suke cajar masu cirewa da tura kudi daga ranar Litinin, 2 ga Disamba, 2024, yanzu babu zancen biyan N100 a kan N10,000.
Sun kara farashin ne sakamakon fara aiwatar da harajin EMTL na N50 a kan duk N10,000 da aka turawa bankunan intanet irinsu Opay, Palmpay, da sauransu.
Harajin EMTL ya shafi sana'ar POS
Masu sana'ar POS sun ce sun ƙara kuɗin cajin su da kashi 25% sakamakon fara aiwatar da harajin EMTL a bankunan intanet a cewar rahoton Legit.ng.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun bayyana cewa duk kudin da ya kai ko ya haura N10,000 da aka aika zuwa asusunsu zai janyo karin N75 saboda harajin EMTL zai shafi asusunsu.
Masu POS sun ce idan sun karɓi sakon kudi daga abokan cinikinsu, suna biyan N50 a matsayin harajin EMTL, wanda dole zai shafi farashin da suke caja.
Masu POS sun kara kudin ladar aiki
Sun bayyana cewa dole ne su sanya harajin EMTL a cikin kudin da za suke karba daga abokan huldarsu ma damar suna son samun riba.
Olugbenga Toki, wani mai POS, ya shaida wa Legit.ng cewa sun fara aiwatar da sabon farashin tun Litinin, 2 ga Disamba, lokacin da suka samu sanarwa daga bankunan.
“Duk wanda ya zo cirar kudi ko turawa, ina fada masa cewa an canja farashi yanzu, wasu na fahimta wasu kuma suna hakura su yi gaba."
Rashin wadatar kudi ya jawo karin farashi
Adedayo Adeleke, wani mai PoS a yankin Toyin na Iju-Ishaga, ya ce sun ƙara farashinsu saboda sun fi amfani da bankunan intanet.
“Na ƙara cajin. Maimakon Naira 100 kan N10,000, yanzu ina karbar N150 ko sama da hakan, amma ya danganta da yawan kudin da za a karba."
Masu PoS sun kuma ce rashin kudi a hannunsu shi ma ya jawo kara farashin la'akari da cewa suna samo kuɗin ne daga kasuwanni, gidajen man fetur, da sauransu.
An fara cirewa 'yan Najeriya harajin N50
Tun da fari, mun ruwaito cewa daga ranar 1 ga Disambar 2024, gwamnatin tarayya ta fara cire harajin N50 kan duk wata N10,000 da aka turawa masu amfani da bankunan intanet.
Gwamnatin tarayyar ta sanar da fara cajar kudin ne a matsayin harajin Electronic Money Transfer Levy (EMTL) da ke a karkashin dokar kudi ta 2020.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng