Sultan da Shugaban CAN Sun Ajiye Bambancin Addini, Sun Mika Bukata 1 ga Tinubu

Sultan da Shugaban CAN Sun Ajiye Bambancin Addini, Sun Mika Bukata 1 ga Tinubu

  • Kungiyar hadin kan addinai ta Najeriya (NIREC) ta bukaci gwamnatin Bola Tinubu ta hukunta masu daukar nauyin ta’addanci
  • Sarkin Musulmi da shugaban kungiyar CAN sun ce arzikin Najeriya ya zama matsala saboda rashin adalci wajen rabon shi
  • Kungiyar NIREC ta kuma koka kan yadda rashin tsaro ya jawo koma baya a Arewa da ma Kudu tare da ba Tinubu shawarar mafita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar NIREC ta bukaci gwamnati ta hukunta masu daukar nauyin ta'addanci da jefa 'yan Najeriya a wahala ba tare da la’akari da matsayinsu ba.

Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III da Shugaban kungiyar CAN, Archbishop Daniel Okoh, sun yi wannan kira a taron NIREC na karshen shekara a Abuja.

Sultan da CAN sun yi magana kan matsalar rashin tsaro a Najeriya
Sultan, CAN karkashin kungiyar NIREC sun nemi Tinubu ya hukunta masu daukar nauyin ta'addanci. Hoto: @presidentofCAN, @NSCIAng, @OficialABAT
Asali: Twitter

'Yan siyasa su guji tara dukiya' - Sultan

Kara karanta wannan

Mummunar gobara ta laƙume kayan miliyoyin Naira a babban birnin jihar Kwara

Shugabannin sun bayyana cewa hare haren 'yan ta’adda ya jefa mutane cikin halin ƙunci, an lalata dukiya tare da tilasta mutane gudun hijira, a cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin Musulmi ya yi kira ga ‘yan siyasa da su guji tara dukiya ta haram, yana mai cewa dukiya ta Allah ce, kuma yana ba da ita domin taimakon talakawa.

Alhaji Sa'ad Abubakar III ya gode wa mambobin NIREC da sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, bisa sadaukarwarsu wajen tabbatar da zaman lafiya a 2024.

Shugabannin Kirista sun koka kan rashin tsaro

Shugaban CAN, Daniel Okoh, ya ce arzikin man fetur da albarkatun ƙasa sun zame wa Najeriya ƙalubale maimakon albarka saboda rashin adalci wajen rarraba su.

Archbishop Okoh ya ce rashin adalci wajen sarrafa albarkatun ƙasa ya haddasa rikici tsakanin ƙabilu da yankuna.

Rabaran Cornelius Omonokhua, sakataren NIREC ya ce albarkatun ƙasa sun zame wa Najeriya masifa maimakon albarka saboda rashin tsaro.

Kara karanta wannan

Tinubu ya saurari kukan jama'a kan ƙudirin haraji, ya ba da sabon umarni

Ya bayyana yadda yankin Neja Delta ke fama da rikicin man fetur, yayin da Arewa ta kasa ci gaba saboda 'yan bindiga da rashin noma.

Sarkin Musulmi ya ba 'yan Najeriya shawara

A wani labarin, mun ruwaito cewa Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ba 'yan Najeriya shawara kan kyautatawa junansu.

A kan turbar kyautatawar, Sarkin Musulmin ya buƙaci ƴan Najeriya masu hannu da shuni da su riƙa raba dukiyoyinsu ga marasa galihu a cikin al’umma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.