NIREC ta yi kira da babbar murya ga Gwamnati ta kare rai da dukiyoyin al’umma
Shugabannin addinin Musulunci da na Kirista sun nuna rashin jin dadinsu game da yadda ake rasa rayuka da dinbin dukiyoyin Bayin Allah a Najeriya.
Jaridar The Nation ta fitar da rahoto a ranar Talata cewa shugabannin sun gargadi gwamnatin tarayya a game da yadda makamai su ke barkowa cikin kasar nan.
Shugaban kungiyar CAN ta Kiristoci, Rabaren Samson Ayokunle da Muhammadu Sa’ad Abubakar III sun yi magana game da lamarin a ranar 4 ga watan Agusta, 2020.
Mai alfarma Sarkin Musulmai da shugaban CAN sun yi jawabi ne wajen wani taron kungiyar NIREC na addinan Najeriya da aka shirya a farkon makon nan.
A matsayinsu na manyan shugabannin Kiristoci da Musulunci na kasa, Sultan da Rabaren Ayokunle sun gabatar da wasu bukatu gaban gwamnati bayan taron.
KU KARANTA: Buhari da shugaabannin tsaro sun yi ganawa ta musamman a Abuja
Wadannan bukatu su ne: Farko, a bankado masu tada kayar baya a Najeriya, a hukunta su. Sannan a karbe makamai daga hannun miyagu.
Bukatar karshe ita ce ayi kokarin hana kowane na’u’in makami yawo cikin Najeriya, wanda da su ne ake amfani wajen yi wa al’umma da dukiyarsu barna.
Kungiyar NIREC ta fitar da wannan jawabi ne ta bakin sakatarenta, Farfesa Cornelius Omonokhua, wanda ya ce su na jin takaicin wannan kashe-kashen da ake yi.
NIREC ta kuma yi Allah-wadai da harin da aka kai wa tawagar gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a garin Baga a kwanakin bayan nan.
Jawabin ya kare da cewa: “Don haka NIREC ta na sake kira ga gwamnati a kowane mataki ta dauki tsaro ya zama babban abin da ke gabanta.” Ta ce dole a tashi tsaye, a kare al’umma.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng