Sheikh Ahmad Gumi Ya Fadi Matsayarsa kan Kudirin Harajin Gwamnatin Tinubu

Sheikh Ahmad Gumi Ya Fadi Matsayarsa kan Kudirin Harajin Gwamnatin Tinubu

  • Sheikh Ahmed Gumi ya bi sahun masu yin magana kan ƙudirin harajin da gwamnatin Bola Tinubu ta kawo a ƙasar nan
  • Malamin addinin musuluncin ya nuna goyon bayansa ga ƙudirin, ya bayyana cewa dokokin suna da amfani a Najeriya
  • Sheikh Gumi ya yi nuni da cewa daga cikin masu sukar ƙudirin, ba su fahimci abin da kundin aka kai majalisa ya ƙunsa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmed Gumi, ya yi magana kan batun ƙudirin haraji da gwamnatin Bola Tinubu ta ɓullo da shi.

Sheikh Gumi ya bayyana goyon bayansa ga ƙudirin, yana mai cewa dokokin suna da amfani ga ƴan Najeriya.

Sheikh Gumi ya yi magana kan kudirin haraji
Sheikh Gumi ya goyi bayan kudirin haraji Hoto: Dr. Ahmed Abubakar Mahmud Gumi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa wasu gwamnoni, ƴan majalisu, da sarakunan gargajiya daga Arewa sun nuna adawa ga ƙudirin, suna masu cewa aiwatar da dokokin na iya ƙara tsananta talauci a yankin.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun saki bama bamai a sansanin 'yan ta'adda, an hallaka myagu masu yawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa waɗannan sababin dokoki guda huɗu an tsara su ne don sauƙaƙa gudanar da haraji, rage nauyin da ke kan masu ƙaramin ƙarfi.

Sheikh Ahmad Gumi ya goyi bayan ƙudirin haraji

Sai dai, duk da sukar da wasu manyan Arewa suke yi kan ƙudirin, Sheikh Gumi ya fito ya nuna goyon bayansa a kai, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Sheikh Gumi ya nuna goyon bayansa ne, bayan ya ce an yi masa bayani dalla-dalla kan yadda dokokin za su yi aiki, kuma ya ce yawancin ƴan siyasar Arewa da suke suka, ba su ma tsaya sun duba ƙudirin ba.

Malamin ya yaba da tasirin dokokin gaba ɗaya, amma ya ce sashe na harajin (VAT) na buƙatar gyara domin magance damuwar da ake nunawa a kansa.

"Ina ganin batun da ake ta ce-ce-ku-ce kan VAT shi ne kaɗai ke buƙatar a sake duba shi, idan ba haka ba, wannan tsari yana da amfani sosai ga kowa."

Kara karanta wannan

Ana batun kudirin haraji, Sarkin Musulmi ya ba 'yan Najeriya shawara

- Sheikh Ahmed Gumi

Isa Pantami ya ba da shawara kan ƙudirin haraji

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi tsokaci kan kudirin gyaran haraji na shugaba Bola Tinubu.

Malamin ya bayyana kudirin harajin a matsayin abin da zai iya sauya tsarin tattara haraji idan aka gyara shi yadda ya kamata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng