Harajin Tinubu: Pantami Ya Bukaci Majalisa Ta Dakata, Ya Fadi Wurare 7 Masu Matsala

Harajin Tinubu: Pantami Ya Bukaci Majalisa Ta Dakata, Ya Fadi Wurare 7 Masu Matsala

  • Sheikh Isa Ali Pantami ya yi kira ga majalisar tarayya da ta dakatar da kudirin dokar gyaran haraji domin sake nazari mai zurfi
  • Tsohon ministan tarayyar ya ce akwai wasu sassa a cikin kudirin da suke bukatar sake nazari da shawara daga masu ruwa da tsaki
  • Farfesa Pantami ya yi nuni da mahimmancin samun amincewa daga dukkanin masu ruwa da tsaki tare da fifita muradun ƙasa a lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi tsokaci kan kudirin gyaran haraji na shugaba Bola Tinubu.

Malamin ya bayyana kudirin harajin a matsayin abin da zai iya sauya tsarin tattara haraji idan aka gyara shi yadda ya kamata.

Pantami
Sheikh Pantami ya bukaci a sake nazari kan kudirin haraji. Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Asali: Facebook

Sheikh Pantami ya wallafa a Facebook cewa kudirin yana da wasu matsaloli da suka haɗa da yiwuwar rashin daidaituwa da kundin tsarin mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan majalisar Arewa sun gana, an dauki matsaya kan kudirin harajin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma bayyana cewa akwai buƙatar yin cikakken nazari kan kudirin tare da samun ra’ayin masu ruwa da tsaki.

Isa Pantami ya ce a dakatar da kudirin haraji

Sheikh Pantami ya shawarci majalisar tarayya da ta dakatar da kudirin gyaran haraji domin ba da dama ga karin tattaunawa.

Ya kuma ce majalisar ba za ta iya magance dukkanin matsalolin kudirin ita kaɗai ba, don haka ya bukaci a haɗa kan dukkanin masu ruwa da tsaki domin samun mafita ta bai ɗaya.

Pantami: Wuraren 7 da ke bukatar sake nazari

Daga cikin sassan da Sheikh Pantami ya nuna suna buƙatar gyara akwai wurare bakwai:

  • Sashe na 3(3), 7(6), 8(2) da 23
  • Sashe na 28, da sashe-sashen 95, 96, 97 da 118
  • Sashe na 141

Gina amana tsakanin gwamnati da ‘yan ƙasa

The Guardian ta wallafa cewa Sheikh Pantami ya yi kira ga gwamnati da ta mayar da hankali kan gina amana tsakanin ta da ‘yan ƙasa, yana mai cewa:

Kara karanta wannan

"Majalisa za ta amince da kudirin haraji kuma babu abin da zai faru," Sanata

"Lamuranmu a ƙasa su na tabarbarewa saboda rashin amincewar da ke tsakanin gwamnati da jama’a."

- Sheikh Pantami

Ya kuma yi kira ga duka matakan gwamnati da su fifita muradun ƙasa fiye da na kashin kansu tare da yin nazarin matsaloli cikin fahimta da adalci.

Majalisa ta daga muhawara kan tsarin haraji

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar wakilai ta Najeriya ta dage tattaunawa kan kudirin gyaran haraji bayan samun matsin lamba daga Arewa.

Sanarwar majalisar ta ce dagewar ta biyo bayan bukatar kara yin shawarwari da masu ruwa da tsaki ne a kan kudirin harajin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng