Sheikh Gumi Ya Nemo Hanyar Yakar Lakurawa, Ya Fadi Masu Daukar Nauyinsu
- Fitaccen malamin Musulunci a jihar Kaduna, Sheikh Ahmed Abubakar Gumi ya ba gwamnatin Najeriya shawara kan Lakurawa
- Sheikh Ahmad Gumi ya ce har yanzu ba a gama tantance ainihin akidar yan kungiyar Lakurawa ba a Najeriya
- Malamin ya bukaci samar da wasu dakaru da ba na hukuma ba domin yakarsu ba kawai sojoji da aka kirkira domin yaki ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Sheikh Ahmed Mahmud Gumi ya yi magana kan yan kungiyar ta'addanci ta Lakurawa a Najeriya.
Sheikh Gumi ya shawarci Gwamnatin Tarayya ta samar da jami'an tsaro na musamman domin yakar yan ta'addan Lakurawa.
Sheikh Gumi ya magantu kan 'yan Lakurawa
Shehin malamin ya bayyana haka ne yayin hira da gidan rediyon Eagle 102.5 FM wanda jaridar Legit ta bibiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Gumi ya ce har zuwa yanzu ba a iya tantance ainihin akidar Lakurawa ba duba da harin da suka kai a Mera da ke jihar Kebbi.
Bayan kisan mutane 17 a Mera, malamin ya ce za a iya cewa ba su da bambanci da sauran yan ta'adda da ke yankin Sahel, New Telegraph ta ruwaito.
Lakurawa na samun taimakon kasashen waje?
"Akwai wadanda ke daukar nauyinsu daga ƙasashen ketare saboda akwai albarkatun kasa da yawa a Najeriya."
"Suna zuwa domin albarkatun kasa inda suke kawo rudani saboda mu nemi kariyarsu daga baya."
- Sheikh Ahmed Mahmud Gumi
Sheikh Gumi ya kawo hanyar gamawa da Lakurawa
Sheikh Gumi ya koka kan kwarewar sojoji, ya ce ba su da cigaban da za su yaki yan ta'adda a halin da ake ciki, cewar rahoton Daily Post.
Ya ce ya kamata a sani jami'an tsaro na wadanda ba na hukuma ba da suke da masaniya kan yankunan ba sojoji da kawai yaki da yan uwansu sojoji suka sani ba.
"An tsara sojojin Najeriya kamar irin na Birtaniya ba wai domin su yaki yan bindiga ba sai dai sojoji yan uwansu."
Lakurawa sun fantsama wasu jihohin Arewa
Kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin kara tura jami'an tsaro yankunan da yan kungiyar Lakurawa suka addaba.
Ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ya tabbatar da haka, ya ce sojojin sama sun yi ruwan wuta kan yan ta'addan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng