Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya, Sun Kashe Ɗan Sanda
- Miyagun ƴan bindiga sun yi garkuwa da tsohon ɗan majalisar wakilan tarayya, Hon. Dr. Joseph Haruna Kigbu a jihar Nasarawa
- Maharan sun buɗe wuta kan matafiya, suka kashe ɗan sanda ɗaya kafin daga bisani su yi awon gaba da ɗan siyasar a hanyarsa ta zuwa Jos
- Mazauna yankin sun tabbatar da cewa wurin da lamarin ya faru ya yi ƙaurin suna wajen yawan hare-haren ƴan ta'adda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Nasarawa - Wasu da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun yi garkuwa da tsohon ɗan majalisar wakilan tarayya, Hon. Dr. Joseph Haruna Kigbu a hanyar zuwa Jos.
An ruwaito cewa maharan sun sace tsohon ɗan majalisar a tsakanin kauyen Nunku a ƙaramar hukumar Akwanga da ke Nasarawa da Gwantu a yankin Sanga a Kaduna.
Jaridar Vanguard ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:00 na yammacin jiya Litinin, 2 ga watan Disamba, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindiga sun sace tsohon ɗan majalisa
Maharan sun kuma hallaka ɗan sandan da ke tare da Dr. Joseph, wanda ya yi koƙarin dakile yunkurin sace tsohon ɗan majalisar.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ƴan bindigar sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi a harin, lamarin da ya firgita masu ababen hawar da suka biyo titin.
Mazauna kauyen sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka kara da cewa wurin ya kasance wurin da ake yawan aikata miyagun laifuka tsawon shekaru.
Ƴan sanda sun yi gum da bakinsu
Kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
An kira layin wayar jami'in hulda da jama'a na rundunar ƴan sanda domin jin ta bakinsa amma bai ɗaga kiran ba.
Garkuwa da tsohon ɗan majalisar tare kashe ɗan sandan da ke ba shi kariya ya ƙara nuna irin yadda yankin ke fama da matsalar tsaro.
Ƴan sanda sun ceto mutum 14 a Nasarawa
A wani labarin, kun ji cewa 'yan banga da masu farauta sun kashe wasu masu garkuwa da mutane a kazamin artabu da suka yi a dajin Achido, Nasarawa.
An ceto mutane 14 bayan daya daga cikin wadanda aka sace ya tsero, sai ya bayyana wurin da masu garkuwan suka ajiye su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng