2025: Gwamna Sule Ya Gabatar da Kasafin N382bn, Ya Fadi Fannin da Zai Samu Fifiko

2025: Gwamna Sule Ya Gabatar da Kasafin N382bn, Ya Fadi Fannin da Zai Samu Fifiko

  • Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule ya gabatar da kasafin 2025 na Naira biliyan 382.5 ga majalisar jihar domin bunkasa tattali
  • Gwamna Abdullahi ya yi bayanin yadda kasafin zai kawo ci gaba a ilimi, gine-gine, lafiya, noma da kuma inganta tsaro a Nasarawa
  • Shugaban majalisar, Danladi Jatau, ya tabbatar da cewa majalisar za ta gaggauta amincewa da kasafin domin amfanin jama'ar jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya gabatar da kasafin Naira biliyan 382.5 na shekarar 2025 ga majalisar dokokin jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa an ware N159.97bn(41.82%) domin ayyukan yau da kullum, sannan an ware N222.60bn (58.18%) domin manyan ayyuka.

Gwamna Abdullahi Sule ya yi bayani yayin da ya gabatar da kasafin Nasarawa na 2025
Gwamnan Nasarawa ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2025. Hoto: @IsuwaSunday
Asali: Twitter

Ilimi ya kwashi kaso mai tsoka a kasafin Nasarawa

An ware N80.14bn ga sashen gudanarwa, N139.84bn ga tattalin arziki, N10.61bn ga shari’a, da kuma N151.97bn ga zamantakewa.

Kara karanta wannan

Bayanai sun fito da kotu ta garkame yan sanda 2 da jami'in hukumar NIS a Gombe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kasafin shekarar 2025 na jihar ya mayar da hankali kan inganta ilimi, gina tituna, noma, lafiya, tsaro, da fasahar zamani domin bunkasa cigaban jihar.

A fannonin gudanarwar jihar, an ware wa ilimi, kimiyya da fasahar zamani N78.16bn, sannan aka ware N71.70bn ga bangaren gine-gine, da kuma N50.75bn ga fannin tsaro.

Abin da noma, jari da matasa suka samu a Nasarawa

A bangaren lafiya an ware N36.20bn, noma da albarkatun ruwa sun samu N36.07bn yayin da kuma muhalli ya samu N27.02bn.

Sauran sassan sun hada da kasuwanci da zuba jari wanda ya samu N26.11bn, yawon bude ido kuma N19.36bn, sai bangaren dokoki da ya samu N10.03bn.

Matasa da wasanni sun samu N9.77bn, inda harkokin jin kai da mata kuma ya samu N6.40bn.

Majalisar Nasarawa za ta amince da kasafin kudin

Shugaban majalisar, Danladi Jatau, ya bayyana cewa za su gaggauta amincewa da kasafin kudin don ganin jihar ta samu cigaba a cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan gwamnati na cikin alheri dumu dumu, gwamna ya fara biyan N72000

Rt. Hon. Jatau ya ce majalisar ta bakwai za ta ba gwamnatin jiha goyon baya don tabbatar da samun dimokradiyya mai amfani ga al'umma.

Ya kuma tabbatar wa Gwamna Sule cewa majalisar dokokin jihar za ta ba wannan kasafi cikakken kulawa.

Gwamnan Legas ya gabatar da kasafin N3trn

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas ya gabatar da Naira tiriliyan uku gaban majalisa a matsayin kasafin jihar na 2025.

Kasafin kudin, wanda aka yi wa take da "Kasafi mai dorewa," ya mayar da hankali kan manyan ayyukan ci gaba don bunkasa tattalin arzikin jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.