Gwamnan Kaduna Ya Tuna da Mutanen Tudun Biri Shekara 1 bayan Jefa Bam a Maulidi
- Gwamnan Kaduna ya kaddamar da ayyuka a kauyen Tudun Biri, shekara guda bayan jefa bama-bamai kan ƴan Maulidi
- Malam Uba Sani ya ce bayan koyar da matasan kauyen sana'o'in da za su dogara da su, gwamnatinsa ta shirya ba su jari
- A watan Disambar bara jirgin sojojin Najeriya ya saki bama-bamai a taron Maulidi wanda ya yi ajalin gomman mutane
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya kaddamar da muhimman ayyukan da za su amfani al'umma a Tudun Biri.
Gwamna Uba ya buɗe asibitin kiwon lafiya a matakin farko (PHC) mai gado 25, cibiyar koyar da sana'o'i da kuma wurin fuda da kula da lafiya ido a ƙauyen.
Wannan dai wani ɓangare ne na cika shekara ɗaya cif bayan kuskuren da sojoji suka yi na jefa bama-bamai kan masu Maulidi a bara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na manhajar X ranar Lahadi, 1 ga watan Disamba, 2023.
Gwamnan Kaduna ya tuna da 'yan Tudun Biri
Bayan buɗe ayyukan, Uba Sani ya kuma raba buhunan 300 na shinkafa mai nauyin kilo 50, buhunan masara 300 da takin NPK buhu 500 ga mazauna Tudun Biri da kauyukan da ke kewaye.
Idan ba ku manta ba mutane sama da 100 suka mutu da jirgin sojoji ya yi kuskuren jefa bama-bamai a taron Maulidi a kauyen Tudun Biri ranar 3 ga Disamba, 2023.
Hakan ya sa gwamnatin Kaduna ta yi alkawarin samar da ababen more rayuwa kamar titi, ruwa, makaranta, asibiti da cibiyar koyar da sana’o’i ga al’ummar kauyen.
Tudun Biri: Gwamnati za ta ba matasa jari
Da yake jawabi bayan kaddamar da ayyukan, Gwamna Uba Sani ya ce gwamnati za ta ba mutasan yankin jari bayan sun kammala koyon sana'o'i.
"Gwamnatinmu ta maida hankali wajen inganta rayuwar al'umma domin ta haka ne kaɗai za ta yi nasarar fatattakar talauci.
"Cibiyar koyon sana'o'i za ta koyawa matasan Tudun Biri sana'o'in da za su dogara da kansu har ma su zama masu ɗaukar ma'aikata."
- Uba Sani.
Gwamnan Kaduna ya naɗa wasu kwamishinoni
Kun ji cewa Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya yi garambawul a gwamnatinsa yayin da ya naɗa sababbin kwamishinoni.
Malam Uba Sani ya naɗa kwamishinonin kuɗi, tsaron cikin gida da harkokin cikin gida a gwamnatinsa kamar yadda aka sanar a makon jiya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng